Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello ya ce ko kadan ba zai amince a yi masa rigakafin cutar COVID-19 ba.
Kalaman nasa na zuwa ne kwanaki kadan bayan rigakafin AstraZeneca ya zo Najeriya kuma a daidai lokacin da ake shirin fara rabawa Gwamnoni a ‘yan kwanaki masu zuwa.
- Kotu ta dakatar da shirya mukabala tsakanin Abduljabbar da malaman Kano
- Duk mai COVID-19 da ya shigo Jihar Kogi zai warke —Yahaya Bello
Sai dai yayin wata tattaunawa da Gidan Talabijin na Channels a cikin shirinsu na ‘Politics Today’, Gwamnan ya ce ba zai lamunci a yi amfani da mutanen jiharsa wajen gwajin rigakafin ba.
“Ba ruwanmu da cutar Coronavirus a jihar Kogi. Muna da abubuwan da suka fi ta muhimmanci a jiharmu.
“COVID-19 wata ‘yar kankanuwar matsala ce daga cikin matsalolin da muke fuskanta a jihar Kogi; mun sami barkewar annobar zazzabin Lassa da kuma ta Shawara kuma mun magance su ba tare da wani surutu ba.
“Iyakar abin da na sani shine ba na bukatar wata rigakafi, babu abin da yake damu na, lafiya ta kalau. Ba zan yarda ayi min kowacce irin rigakafi ba,” inji Gwamnan.
“Muhammdu Buhari shine Shugaban Kasa kuma ina girmama shi sosai, dukkanmu muna kaunarsa saboda yana shugabanci abin kwaikwayo. Idan yana da bukatar ayi masa rigakafin, abu ne mai kyau, amma ni dai ba zan bari ayi min da mutanen jihata ba” inji Gwamna Yahaya Bello.
A ranar Asabar ne dai ake sa ran yi wa Shugaba Buhari da Mataimakinsa Yemi Osinbajo rigakafin a bainar jama’a.