Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rufe kofar yiwuwar sakin shugaban ’yan a-wayen Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu.
Wasu daga cikin shugabannin kabilar Igbo ne dai suka ziyarci Shugaba Buhari, suka roke shi ya sa baki a saki Nnamdi Kanu.
- Buhari ya ayyana ’yan bindiga a matsayin ’yan ta’adda
- Yadda sa’insa kan raken N50 ya kai ga zubar da jini a Kwara
A yayin tattaunawar tasu, shugabannin sun roki Buhari ya tausaya a kan lamarin, shi kuma ya yi musu alkawarin yin wani abu a kai.
Amma a wata hira ta musamman da gidan talabijin na Channels ya yi da shi, Buhari ya ce ba zai yi wa bangaren shari’a katsalandan ba.
“Babu yadda za a yi na shiga hurumin shari’a, lamarin Kanu na gaban kotu amma na yi mamaki lokacin da Kanu yake Turai, yake cin zarafin gwamnatin nan, na dauka zai iya zuwa ya kare kansa.
“Don haka, mun ba shi dama don ya kare kansa game da gwamnatinmu, ba wai ya rika cin zarafi daga Turai ba kamar ba dan Najeriya ba. Gara ya zo nan ya rika kalubalantar mu.
“’Yan Najeriya sun san ba na shiga sha’anin da ya shafi shari’a, don haka wadanda suke cewa a sake shi, to su sani ba za mu sake shi ba.”
Kada ku jira sai gwamnati ta ba ku aiki —Buhari ga matasa
Kazalika, Buhari ya gargadi matasan Najeriya cewa su bar dogara sai gwamnati ta ba su aiki idan suka kammala karatu.
Idan za a iya tunawa, a shekarun baya Shugaba Buhari ya sha suka bayan da ya bayyana matasan Najeriya a matsayin ‘malalata’.
Da aka yi masa tambaya game da tunaninsa a kan matasan kasar nan, Buhari ya ce, “Ina fatan idan sun je makaranta, sun yi aiki tukuru, sun kammala digiri dinsu, kada su tsaya jira cewa sai gwamnati ta ba su aikin yi.
“Ka samu ilimi ne saboda ka fi wanda ba shi da ilimi. Don haka smun ilimi ba ya nufin ka dogara sai gwamnati ta sama maka aikin yi, kamar yadda turawan mulkin mallaka suka gadar mana, ka mallaki mota, da gida sannan ka rika aiki daga karfe 8 na safe ka tashi 2 na rana ba.”
Da aka tambaye shi kan zaben 2023, ya ce wannan ba damuwarsa ba ce, ba zai bayyana wanda zai gaje shi idan ya bar mulki a 2023 ba.