Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya ce gwamnatinsa ba za ta yi kasa a guiwa ba wajen ganin an samu zaman lafiya da tsaro a kasar nan.
Buhari ya bayyana haka ne a ranar Litinin, yayin bikin cika shekara 58 da kafuwar rundunar Sojin Saman Najeriya a Jihar Kano.
- An gano nau’in sauron da ba ya jin maganin Maleriya a Jigawa
- NAJERIYA A YAU: Yadda Dokar Zabe Ta Tantance Daliget
Shugaba Buhari ya ce gudunmawar da gwamnatinsa ta bai wa rundunar sojin saman, ya taimaka wajen yaki da ‘yan bindiga.
Ya yi alkawarin zai ci gaba da bai wa rundunar sojin saman dukkanin gudunmawar da ta ke bukata wajen yaki da ‘yan ta’adda a fadin kasar nan.
“Irin makudan kudaden da muka zuba sun taimaka wajen yaki da ’yan ta’adda da bata-gari a jihohi.
“Za mu ci gaba da tallafawa rundunar sojin saman kasar nan. Kuma ina bada tabbacin cewar gwamnatina za ta yi duk mai yiwuwa wajen bada kwarin guiwar kawo karshen matsalar tsaro.
“Wannan gwamnati ba za ta saduda ba har sai an samu zaman lafiya da tsaro a kasar nan. Don haka ina son sanar da ku cewar ku zama cikin shiri, ku zage damtse don tabbatuwar hakan.”
A watan da ya gabata ne kungiyar Dattawan Arewa ta bukaci Buhari ya yi murabus kan gaza kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi wasu yankunan kasar nan.
Sai dai Buhari ya mayar wa da kungiyar martani cewar, yin murabus ba zai magance matsalar tsaro a kasar nan ba.