Tsohon Gwamnan Jihar Benuwe, Samuel Ortom, ya karyata rade-radin da ake yadawa cewar zai fice daga jam’iyyar PDP.
Ortom, ya bayyana haka ne yayin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP a ranar Litinin a Makurdi.
- Gobara ta kone shaguna 50 a kasuwar ’yan Katako a Kano
- Gaza: Sojan Amurka ya kona kansa a ofishin jakadancin Isra’ila
Tsohon gwamnan, ya ce zai ci gaba da zama dan jam’iyyar kuma zai ci gaba da yin aiki don ci gabanta.
“Ba zan koma wata jam’iyyar siyasa ba. Ba zan je ko ina ba. Zan ci gaba da zama a jami’yyar PDP.
“Na taimaka wajen gina jam’iyyar kuma zan yi aiki tukuru wajen ci gabanta,” in ji Ortom.
Ya bukaci shugabannin jam’iyyar a jihar, da su zakulo masu yada jita-jita saboda barnar da hakan ke yi.
Da yake jawabi a wajen taron, Sanat Gabriel Suswam, ya shawarci shugabannin jam’iyyar PDP da su ci gaba da kokarin hada kai don kara karfafa jam’iyyar.
A cewarsa, PDP na iya lashe dukkan zabukan da ke tafe a jihar.
Suswam, wanda tsohon gwamnan jihar ne, ya yi alkawarin cewa jam’iyyar ba za ta fifita kowa ba, face kokarin dinken barakar da ke cikinta.
Ya ce PDP ta tafka kurakurai a lokacin babban zaben 2023, kuma jam’iyyar ta koyi darusa masu tarin yawa.
Tsohon gwamnan ya ce darusan da jami’yyar ta koya za su zaburar da ita don kafa tsari mai kyau da kuma goga wa da jami’yyar APC mai mulki.
Shugaban PDP na jihar, Mista John Ngbede, ya bukaci masu haifar da rikici a jami’yyar da su yi taka-tsan-tsan.
Ngbede, ya ce idan suka ci gaba da haifar da rashin jituwa tsakanin shugabanninta za su fuskanci hukunci.
“Mu shugabannin PDP muna da hadin kai kuma za mu ci gaba da kasancewa tare a ko da yaushe.
“Za mu yi aiki tukuru don lashe zabe a 2027. Gidan gwamnatin jihar Benuwe namu ne,” in ji Ngbede.