✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba zan dawo da tallafin man fetur ba — Tinubu

Mataki ne mai tsauri amma ya zama tilas domin farfaɗo da tattalin arziki Nijeriya.

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ba zai dawo da tallafin man fetur ba.

Tinubu ya ce duk da cewa cire tallafin man fetur ɗin mataki ne mai tsauri, sai dai ya zama tilas domin farfaɗo da tattalin arziki ƙasar.

Shugaban na wannan furuci ne a yayin jawabinsa ga al’ummar kasa kai tsaye a safiyar wannan Lahadin.

Wannan na zuwa bayan da matasa suka fara wata zanga-zangar gama gari a faɗin ƙasar a ranar Alhamis 1 ga watan Agusta kan tsadar rayuwa da sauran matsaloli da su ke addabar kasar.

Matasan dai suna kokawa kan tsadar man fetur, wutar lantarki, kayan masarufi da dai sauran su, inda suke ta kiraye-kiraye da gwamnatin ta dauki matakai na kawo mafita daga wannan mawuyacin hali da al’ummar kasar take fuskanta na fatara da talauci.

Sai dai sabanin buƙatun masu zanga-zangar tsadar rayuwa ta #EndBadGovernance, Tinubu ya yi watsi da batun dawo da tallafin man fetur.

A cewarsa, “tsawon gomman shekaru tattalin arzikinmu ya kasance mai ƙarancin ƙima da rashin daidaito saboda wasu manufofi waɗanda suka kawo cikas ga ci gabanmu.

“Sama da shekara guda ke nan Nijeriya ta kai matsayin da ba za mu iya ci gaba da amfani da hanyoyin wucin gadi don magance matsalolin da suka daɗe suna addabar ƙasar ba.”

Shugaban ya kuma shaida wa masu zanga-zangar cewa jami’an tsaro za su ci gaba da tabbatar da cikakken tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba ta hanyar da ta dace.

Ya kara da cewa “Dimokuradiyyarmu za ta ci gaba ne idan aka mutunta da kuma kare hakkokin da Kundin Tsarin Mulki ya ba kowane ɗan Najeriya.”