✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba za mu yarda a sayar da kuri’unmu da sunan karba-karba ba – Sheikh Jingir

“Don haka, kada mu yarda kuri’armu su zama na banza."

Shugaban Majalisar Malamai ta Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta Kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir, ya ce ba za su taba yarda wani dan siyasa ya je ya sayar da kuri’unsu da sunan tsarin karba-karba a zaben 2023 ba.

Sheikh Sani Yahya Jingir, ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da wa’azi a wajen taron Wa’azin Kasa da kungiyar ta shirya a garin Jingir,a karshen makon jiya.

Ya ce “Kada mu yarda wani dan yisasa ya je ya sayar da kuri’unmu ya ce a yi karba-karba a Najeriya, domin tsarin karbakarba wata irin muguwar caca ce. Kuma mutum ya mayar da mutane kamar kayansa ke nan.

“Mu ba kayan wadansu ’yan siyasa ba ne, mu mallakar Ubangiji ne. Idan ka ga Shugaban Kasa ko Gwamna ko wani dan majalisa a Najeriya da kuri’armu muka zabe shi.

“Don haka, kada mu yarda kuri’armu su zama na banza, wani ya je ya ba wanda ya ga dama.

“Mu ne za mu zabi wanda muke so, idan mun hangi yana da manufofi masu kyau na raya ilimi da kawo tsaro da raya al’umma da bunkasa noma,” inji shi.

Sheikh Jingir ya yi kira ga ’yan Najeriya su zabi mutanen kirki masu gaskiya da rikon amana, a zaben shekara ta 2023, maimakon zabar mutane marasa imani da suke mantawa da al’ummarsu.