Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya ce ’yan bindiga ’yan ta’adda ne da ya dace a kawo karshensu.
Ya bayyana hakan ne yayin ziyarar barka sa Sallah da Babban Hafsan Sojin Kasan Najeriya, Janar Faruk Yahya ya kai masa har Fadarsa da ke Sakkwato.
A cewarsa, “Ba za mu taba bari ‘yan ta’adda su samu wani sukuni ba, don haka akawai bukatar sabunta tsare-tsaren da za a ci galaba a kansu.”
Ya ce da zarar an sabunta dabarar yaki, za a samu nasarar kawo karshensu.
Kazalika, Sarkin Musulmin, ya bayyana cewar wadannan matsaloli na kara karfin dakarun Najeriya, don suna ba su damar gwada basirarsu ta yaki.
“Kamar yadda shugaban kasa ya sanar a ranar Idin sallah, ni kaina na yarda cewar mun kusa kawo karshen wadannan matsaloli,” in ji shi.
A nasa bangaren, Babban Hafsan Sojin Kasan, ya sha alwashin ganin kasurgin dan bindigar nan Bello Turji da sauran ‘yan bindigar da suka addabi wasu yankunan Arewa maso Yammacin kasar sun shiga hannu.
Da ya ke jawabi a wajen kaddamar da ginin sansanin ‘yan ta’adda a Karamar Hukumar Isa ta Jihar Sakkwato, ya tabbatar da cewa ba za su ragawa ‘yan ta’adda ba.
“Za mu gano maboyarsu, sannan za mu kawo karshensu mu kuma kwato makamansu.”
A cewarsa, makasudin kafa sansanin shi ne don gano inda maboyar ‘yan bindigar take.
“Mun san irin muhimmancin da Isa take da shi wajen shirinmu. Tana rike da wani rukuni mai girman gaske wajen kaddamar da ayyukanmu.
“Muna kafa irin wadannan wurare ne don mu inganta yakin da muke yi da ‘yan ta’adda da bata-gari don mu kawo karshensu da makamansu,” a cewarsa.
Ya kara da cewar za a sake jibge makamai da a sansanin don inganta yaki da ‘yan bindigar.
Ya yaba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari, kan irin yadda ya ke ba su goyon baya a yakin da suke gwabzawa da ‘yan bindiga.