✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba za mu sassauta wa masu yi wa Annabi batanci ba — Gwamnan Sakkwato

Addininmu bai lamunci mu dauki doka a hannu ba don haka mu kasance masu bin koyarwar addinin.

Gwamnan Jihar Sakkwato Dokta Ahmed Aliyu Sokoto ya yi kira ga jama’ar jihar da su ci ga gaba da zaman lafiya tare da kiyaye bin doka da oda.

Gwamnan ya yi wannan kiran ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Abubakar Bawa ya fitar dangane da farmakin da aka kai wa wani Usman Buda Mai Hanji da ake zargin ya yi kalaman batanci ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. a babbar mayanka ta Sakkwato da safiyar Lahadi.

Gwamnan ya yi kashedi ga jama’ar jihar da su kiyeye duk wani yunkuri ko kalami da zai iya taba kima da darajar Manzon Allah, musamman ma dai a gari irin Sakkwato wanda gari ne na musulmai.

Gwamnan ya bayyana cewa mutanensa na da matukar soyayya da kauna ga Annabin Rahama ta yadda ba za su yi wasa da taba janibinsa ba, kan haka ya bukaci al’umma da su ci gaba da mutunta wannan kauna da suke yi.

“Ina kira ga al’ummar jihar nan da mu guji daukar doka a hannu, a maimakon haka su rika kai rahoton duk wani laifi ko zargin batanci ga hukumomi don yin abinda ya dace.

“Addininmu bai lamunci mu dauki doka a hannu ba don haka mu kasance masu bin koyarwar addinin,” inji gwamnan.

Dokta Aliyu ya kara da cewa gwamnatinsa ba za ta taba daukar batun yin batanci ga fiyayyen halitta da sassauci ba, yana mai cewa za ta tabbatar an hukunta duk wanda aka kama da yin batanci ga fiyayyen halitta a bisa ga tanadin shari’ar musulunci.

Kazalika, ya ba da tabbaci cewa a shirye gwamnatinsa take don ganin ta kare rayuka da dukiyoyin al’ummar ta.

Gwamnan ya kuma ja kunnen masu neman ta da zaune tsaye da su daina domin a cewarsa Jihar Sakkwato ba wurin da za a yi wa doka karan tsaye ba ne a kwashe lafiya.

Rundunar ’yan sandan Jihar Sakkwato ta tabbatar da mutuwar mutum daya wanda ake zargi da yin bataci ga Annabi Rahama bayan fusatattun jama’a sun yi masa jina-jina kuma a karshe rai ya yi halinsa a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usman Danfodiyo.

Cikin bayanin da mukaddashin jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASP Ahmad Rufa’’i ya fitar, ya nemi mutane su ci gaba da gudanar lamurransu bisa doka ba tare da fargabar komai ba.

Ya kuma kara da cewa, za su ci gaba bincikar lamarin kuma duk wanda aka samu yana da hannu zai fuskanci fushin doka.