✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajji: Yadda Saudiyya ta tsara jigilar alhazai a minti 15

Maniyyata sama da miliyan biyu daga kasashe kimanin 160 ne za su yi aikin Hajji bana.

Hukumar Aikin Hajji da Umrah ta Kasar Saudiyya ta bullo da sabbin matakai domin saukaka wa mahajjata tafiya a ranakun aikin Hajji.

Gwamnatin Saudiyya ta ce bisa tsarin da hukumar ta yi, tafiyar alhazai daga filin Arfa zuwa Muzdalifa ba zai wuci minti 15 ba, sabanin yadda a baya akan shafe sa’o’i a kan hanyar da ba ta wuci tafiyar ’yan mintoci ba.

A wata ganawa da ta yi da malamai da sauran masu ruwa da tsaki a aikin Hajji daga Najeriya a birnin Makkah, hukumar ta bayyana cewa bana za a yi jigilar alhazai ne a rukuni-rukuni, wanda hakan zai saukaka musu tafiyar, da kuma kawar da cinkoson ababen hawa a hanyar.

Kazalika, bayan dawowa Muna daga Muzdalifa, alhazai za su yi jifa ne a cikin rukuni-rukuni, kuma za a takaita lokacin tsayuwarsu a wurin yin jifa (Jamarat), bayan sun kammala.

Ana sa ran hakan zai magance samun cinkoson jama’a da kuma irin turereniyar da ta yi ajalin daruruwan alhazai a wurin yin jifa shekarar 2015.

Hukumar ta ba da tabbacin cewa ta kammala duk tsare-tsaren da ya kamata domin samun nasara daga bangarenta.

Ta ce amma, hakan zai yi nasara ne kawai idan alhazai da hukumomin aikin Hajji sun ba da hadin kai wajen tabbatar da ganin alhazansu sun bi tsarin.

Don haka abin da ya rage shi ne bangaren hukumomin aikin Hajjin kasashe, don haka duk kasar da ta bari aka samu matsala daga bangaren alhazanta, to kada ta zargi Saudiyya.

A kan haka ne suka ja hankalin masu ruwa da tsaki da su yi duk abin da ya kamata, domin cim-ma wannan buri ta hanyar wayar da kan mahajjata.

A nata bangaren, Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta ba da tabbacin yin iya kokarinta na ganin alhazan Najeriya sun bi tsarin sau da kafa domin a samu biyan bukata.

Hajji mafi girma bayan COVID-19

Ma’aikatar ta ce maniyyata sama da miliyan biyu daga kasashe kimanin 160 ne za su yi aikin Hajji bana.

Karon farko ke nan da aka samu yawan mahalarta aikin Hajji kamar haka, tun bayan da annobar COVID-19 ta sa kasar Saudiyya takaita adadin kujerun Hajjin da take ba wa kasashe.

Kasashe da dama sun tabbatar cewa a wannan karon Saudiyya ta ba su adadin kujerun da ta saba ba su kafin COVID-19.

Mataimakin Ministan Aikin Hajji da Umrah, Dokta Abdel-Fattah Mashat, ya ce ma’aikatar za ta ci gaba da amfani da matakan da ta saba bi, wajen bayar da kujerun Hajji ga kasashe.

Haka kuma ta yi shirin ko-ta-kwana a bangaren kula da lafiya da zirga-zirga da sauran abubuwan da suka shafi alhazai, don samun nasara.

Yadda za a yi Hajjin bana

A daren Lahadi, 7 ga watan Zhul-Hajj ake sa ran fara kwasar mahajjata daga Makka zuwa Muna, wanda ake sa ran kammalawa a ranar Litinin 8 ga wata —Ranar Tarwiya.

Aikin Hajji na farawa ne ranar 8 ga watan Zhul-Hajj, inda alhazai ke taruwa a sansaninsu da ke Muna a Kasa Mai Tsarki.

Washegari 9 ga wata kuma za su hallara a Filin Arfa domin tsayuwa na tsawon yinin ko wani yankinsa, gwargwadon abin da ya samu, suna yin zikiri da addu’o’i da sauran nau’ikan ibada.

Kafin faduwar rana za su wuce Muzdalifa su kwana.

10 ga wata kuma — Ranar Sallar Layya — da hantsi za su koma Muna, inda za su yi jifa da aski da kuma yanka hadayarsu.

Daga nan sai Dawaful Ifada da Sa’ayi da kuma karashen jifa kafin su baro Muna zuwa Makkah.

A karshen aikin Hajji kuma sai Dawafin Bankwana kafin su koma garuruwansu.