Babbar Kotun Jihar Kano da ke zamanta a Miller Road, ta yi fatali da karar da wasu daliban Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, suka shigar gabanta kan neman daukaka kara game da hukuncin da aka yanke wa malamin.
Tun da farko daliban malamin karkashin jagorancin Malam Musa San Turaki Falali sun nemi kotun ta sanya su a jerin masu kara.
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 2, sun sace manoma a Neja
- NAJERIYA A YAU: Tallafin Da ’Yan Najeriya Ke Bukata
Da yake yanke hukunci, Alkalin Kotun Mai sharia Sanusi Ado Maaji, ya yi watsi da karar.
Alkalin kotun, ya bayyana cewa daliban ba sa cikin masu karar tun a kotun kasa har zuwa lokacin da kotun za ta yanke hukunci.
Lauyan masu kara Barista Hashim Hussaini Fagge, ya bayyana cewa za su yi nazari game da hukuncin, domin daukar mataki na gaba.
Idan ba a manta ba kotun Shari’ar Muslunci da ke Kofar Kudu a jihar ce, ta yanke wa Abduljabbar hukuncin kisa bayan samun sa da laifin kalaman batanci ga Annabi Muhammad SAW.
Sai dai daliban malamin sun kuduri niyyar daukaka kara don ganin an sauya hukuncin da kotun ta zartar wa malamin.