Wata bakuwar cuta da ke hallaka kanaan yara ’yan tsakanin shekara hudu zuwa 13 ta bulla a Jihar Sakkwato.
Cutar da kawo yanzu ta yi ajalin mutane takwas, wasu 208 suka nuna alamun kamuwa da ita da suka hada da ciwon ciki, zazzaɓi da kuma matsananciyar rama.
Dokta Ibrahim Usman, Manajan Cibiyar Yaki da Cututtuka ta Najeriya (NCDC) a Sakkwato ne ya bayyana haka a tattaunawarsu da ma’aikatar kafiya ta jihar a gaban Darakta Janar na NCDC, Dokta Jide Idris, tare da tawagarsa ranar Alhamis.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa, lamarin ya faru ne a kananan hukumomin Sabon Birni da Isa na jihar.
Dokta Ibrahim Usman ya ce hukumar NCDC da Gwamnatin Jihar Sakkwato sun dauki matakan dakile yaduwar cutar cikin gaggawa, sun kuma dauki samfurin cutar zuwa manyan dakunan gwaje-gwaje don tabbatar da wace irin cuta ce.
“Tuni, NCDC ta aike da Tawagar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NRRT), don hada kai da Ma’aikatar Lafiya ta jiha don bincikar lamarin.”
Ya kara da cewa, an kai yaran da abin ya shafa asibitin kwararru da ke Sakkwato domin yi musu magani, yayin da jami’ai ke aikin wayar da kan mazauna yankunan da lamarin ya shafa kan illolin wannan cuta tare da ba su shawarwari kan yadda za su kai rahotonta.
Dokta Larai Tambuwal, Babban Sakatariya a Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta Jihar Sakkwato (SSPHCDA) ta shaida wa tawagar da suka ziyarce su cewa ana zargin an samu matsalar ne a harkar noma, wurin kayayyakin da ake amfani da su kamar taki da magungunan kwari.
Babban Daraktan Hukumar Kula da Ayyukan Asibitoci a Jihar Sakkwato, Dokta Bello Attahiru, ya ba da tabbacin daukar karin matakan dakile cutar da kuma kula da wadanda suka kamu da ita.