✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wata Bakuwar Cuta Ta Yi Ajalin Mutane 45 A Kano

Mata da ƙananan yara da tsoffi 45 sun rasu a makonni biyu da suka gabata a karamar hukumar Kura.

Kawo yanzu ana fargabar mutane 45 ne suka rasa ransu sakamakon barkewar wata bakuwar cuta a kauyen Gundutse da ke Karamar Hukumar Kura a Jihar Kano.

Rahotanni na bayyana cewa wadanda lamarin ya rutsa da su, galibinsu mata ne da yara kanana da kuma tsofaffi.

Cutar dai na farawa ne da alamun cutar zazzabin cizon sauro, gudawa, da amai sai mutuwa.

Lamarin ya fara firgita mazauna yankin ne bayan sun ga akalla mutane biyar na mutuwa daga kusan cuta iri ɗaya a duk rana.

Sun bayyana damuwarsu game da karuwar mace-macen fuju’a a cikin makonni biyun da suka gabata, inda da farko suka danganta su da zazzabin cizon sauro ko zafi.

Yawan mace-macen na nuni da cewa an samu barkewar wata cuta da ba a san ta ba a yankin.

Abu Sani, wani mazaunin garin da ya rasa ’ya’ya biyu, ya ce da farko sun yi tunanin cutar zazzabin cizon sauro ce ke damun wani dansa mai shekara biyu, kuma duk wani abu da ya kamata likitoci su yi, sun yi amma yaron ya mutu.

Ya ce, bayan mako guda kuma, wani dan nasa ya kara kamuwa, wanda daga bisani shi ma ya ce ga garinku nan.

Hajara Abubakar, wadda ke jinyar sa a asibiti, ta ce, “Sama da makonni biyu mutane ke mutuwa a nan sakamakon wani irin ciwo da ba mu sani ba. Ya zuwa yanzu, na san mutane 40 da suka mutu.”

Jami’an lafiya a asibitin na Gundutse sun shaida wa wakilinmu cewa kawo yanzu an samu rahoton mutuwar mutane 20.