✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’ar Bayero ta yi wa dalibai karin kudin makaranta

Jami’ar ta Bayero ta bayyana cewa karin zai soma aiki ne a zangon karatu na 2022/2023.

Jami’ar Bayero da ke Kano ta kara kudin makarantar sabbi da kuma tsofaffin dalibai masu karatun digiri na farko da na biyu.

Jami’ar ce ta wallafa wata sanarwa a shafinta na Facebook dauke da bayanai kan yadda karin kudin makarantar ya shafi tsangayoyi daban-daban.

Wannan karin yana zuwa ne makonni bayan gwamnatin Najeriya ta sanar da fito da tsarin bai wa dalibai bashin kudin karatu mara kudin ruwa, wanda tun a lokacin aka soma hasashen cewa za a yi karin kudin makaranta a fadin kasar.

A cikin sanarwar da ta fitar mai dauke da sa hannun mukaddashiyar magatakardanta, Amina Umar Abdullahi, bayan kammala taron Majalisar Gudarwarta karo na 405 wanda ta ce ta gudanar a ranar Litinin, 19 ga watan Yuni, Jami’ar ta Bayero ta bayyana cewa karin zai soma aiki ne a zangon karatu na 2022/2023.

Daliban tsangayoyin koyar da Fasaha da Addinin Musulunci da Shari’a da Ilimin Zamantakewa da Kimiyyar Gudanarwa za su rinka biyan naira 95,000 a matsayin kudin makaranta a duk shekara sa’annan sabbin dalibai a tsanagayoyin za su biya naira 105,000.

Daliban tsangayoyin koyar da Aikin Banki da Hada-Hadar Kudi da Lissafin Kudi za su koma biyan naira 97,000 inda sabbin dalibai kuma su biya naira 107,000.

Dalibai daga tsangayoyin koyar da Ilimin Kwamfuta da Sadarwa da Kasa da Muhalli za su rinka biyan naira 100,000 sai kuma sabbin dalibai su biya 110,000.

Dalibai daga tsangayar koyar da Ilimin Sinadaren Kasa da kuma tsangayar koyar da Tsara Taswirar Birane za su koma biyan naira 105,000 sa’annan sabbin dalibai su biya naira 115,000.

Baya ga kudin makaranta, Jami’ar ta kara kudaden da ake biya na dakunan kwanan dalibai.

A cewar sanarwar, dakin dalibai maza mara gado da katifa ya koma naira 37,590, sai kuma daki mai gado da katifa 57,590.

Sai kuma dakin dalibai mata mai gado da katifa ya koma 80,090. Sa’annan dakin kwanan dalibai na mata ’yan ajeriya masu digiri na biyu ya koma naira 200,000, sai kuma na mata wadanda ba ‘yan Nijeriya ba ya koma 200,000.

Dakin maza kuwa ’yan Najeriya masu digiri na biyu ya koma naira 150,180 sai kuma wadanda ba ’yan Najeriya ba 300,000.