Hukumar Zabe Ta Kasa (INEC), ta ce ba za ta sake tsawaita wa’adin mallakar katin zabe ba, bayan cikar wa’adin a ranar 31 ga watan Yulin 2022.
Kwamishinan Hukumar mai kula da sashen Ilimantar da Al’umma kan mallakar katin, Festus Okoye ne ya bayyana hakan.
A cewar Mista Okoye, sun bai wa jama’a duk wani isasshen lokacin da suke bukata don mallakar katin zaben.
- ASUU ta tsawaita yajin aikin jami’o’in Najeriya da mako hudu
- Zelenskyy ya wajabta kwashe mutane daga Donetsk bayan Ukraine ta kashe sojojin Rasha
Ya ce ba za su sake tsawaita lokacin yankar rajistar ba, duba da yadda lokaci ke kure musu.
INEC ta ce tana so ta mayar da hankali ne ga sauran ayyukan da ke kan jadawalin zaben 2023, kuma dole sai ta rufe yankar katin ne za ta iya samun ci gaba.
A ranar 28 ga watan Yuni ne INEC ta sanar da tsawaita lokacin yin rajistar zuwa ranar 31 ga watan Yulin 2022, bayan bukatar hakan daga bangarori daban-daban na kasar nan.
Har yanzu dai akwai jama’aer kasar da ke bukatar yankar katin zabe, don samun damar kada kuri’a a zaben 2023.