Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin cewa duk rintsi kada a biya waɗanda suka yi garkuwa da ɗaliban Kuriga kuɗin fansa.
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris ne ya bayyana haka bayan taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya da aka gudanar a Aso Rock ranar Laraba.
Ministan ya ce gwamnati ba za ta biya ko sisin kobo ba a matsayin fansa ga maharan don sakin ɗaliban.
Ministan ya ce gwamnatin ƙasar ba za ta lamunci ci gaba da sace ɗalibai don yin garkuwa da su ba.
Saboda haka a cewar ministan, gwamnati ke kira ga jami’an tsaron da su yi duk abin da ya kamata don tabbatar da sakin ɗaliban da sauran mutanen da ke hannun ’yan bindiga a faɗin ƙasar.
“Idan ta kama gwamnati za ta yi amfani da ƙarfin tuwo wajen kuɓutar da ɗaliban nan, saboda hukumomin tsaronmu a shirye suke ko me za a yi a dawo da waɗanna ɗaliban,” in ji shi.
A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne wasu ’yan bindiga suka kai hari makarantar firamare da ƙaramar sakandiren Kuriga, inda suka sace ɗalibai fiye da 200.
Haka kuma akwai wasu mutane 16 da aka yi garkuwa da su a Gonin Gora da ke Jihar Kaduna.
Yayin da masu garkuwa da mutanen Gonin Gora su 16 ke neman kuɗin fansa Naira miliyan 40 da motocin Hilux 11 da babura 150 domin a sako su, har yanzu babu wani labari game da ’yan bindigar da suka sace ɗaliban makarantar Kuriga.
Haka kuma, a Jihar Sakkwato, ’yan bindiga sun yi awon gaba da wasu mutane 15 a ƙauyen Gidan Bakuso, yayin da wasu mata kusan 50 aka ruwaito mayakan Boko Haram sun sace a Jihar Borno.