✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba yanzu za a dawo da lantarki a Arewa ba —TCN

Hukumomin tsaro sun gargaɗi kamfanin TCN kan haɗarin shiga yankin da aka lalata manyan turakun lantarki da ya jefa Arewa cikin duhu

Kamfanin Samar da Wutar Lantarki a Nijeriya (TCN) ya ce babu takamaiman lokacin dawo da wutar lantarki da aka ɗauke a sassan yankin Arewa ba.

TCN ya ce duk da cewa ana ƙoƙarin gyara wutar, amma matsalar rashin tsaro ta sa ba za a iya ci gaba da aikin gyaran ba.

Babbar jami’ar TCN, Nafisatu Asabe Ali, ta ce kamfanin ya samu takardar gargaɗi daga Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro cewa akwai haɗarin gaske shiga yankin da aka lalata manyan turakun lantarki uku, saboda matsalar rashin tsaro.

Ta ce ci gaba da cewa duk da cewa kamfanin ya riga ya tanadi kayan aikin gyaran, amma ba zai iya shiga wajen ba, sai ya ki daga hukumomin tsaro.

Kimanin kwanan huɗu a jere ke nan da aka ɗauke wutar bayan lalacewar babban layin lantarkin Shiroro zuwa Manzo, wanda ke isar da wutar ga akasarin yankin Arewa.

Bayan lalacewar layin ne TCN ya yi ƙoƙarin amfani da layin Ugwaji zuwa Apir zuwa .mai karfin 330kV domin tura wuta zuwa yankin, amma aka yi rashin sa’a shi ma ya lalace.

TCN ya bayyana cewa matsalar ta jefa jihohin Arewa maso Gabas da arewa maso Yamma da wani yanki na Arewa ta Tsakiya cikin duhu.

Injiniya Nafisa ta bayyana cewa har yanzu babban layin Shiroro ba ya aiki, kuma ba za a iya cewa ga takamaiman lokacin da za a gyara shi ba saboda matsalar tsaro.

Ta ci gaba da cewa ko da an gyara layin Ugwaji zuwa Apir mai karfin 750, ƙarfin wutar da zai iya dauka a yanzu bai wuce 350kV.

Don haka sai dai a ba wa wasu yankunan jihohin Kano da Kaduna da Jamhuriyar Nijar.