Tsohon Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi ya ce Allah ya yi masa baiwar da ba wani dan Najeriya da ya taki irin sa’ar da ya samu.
Sarki Sanusi wanda kuma shi ne Halifan Darikar Tijjaniyya na Najeriya, ya bayyana hakan ne yayin wani taron gabatar da makaloli na shekara-shekara da aka gudanar kan cikarsa shekara 60 a duniya a ranar Asabar.
Bayanai sun ce a gudanar da taron ne a dakin taro na Umaru Musa ’Yar Adu’a da ke Jihar Kaduna.
Sasshen Hausa na BBC ya ruwaito cewa, taron shi ne irinsa na farko kuma ana sa ran za a ringa gudanar da shi duk shekara.
A wajen taron, masana sun gabatar da makaloli kan irin sauye-sauyen da Sarki Sanusi ya kawo a wuraren da ya samu damar yin aiki.
A jawabinsa, Sarki Sanusi ya ce idan ya yi waiwaye ya dubi shekaru 60 da ya yi a duniya, yana shiga halin damuwa da kunci, saboda yadda aka samu koma-baya a bangarorin rayuwar Najeriya.
Ya ce ya zama Shugaban bankin kasuwanci, daga nan ya zama Gwamnan Babban Bankin Najeriya, ya zama Sarkin Kano, sannan yanzu ya zama Halifan Darikar Tijjaniyya na Najeriya.
“Babu wani dan Najeriya da ya samu irin wadannan damarmaki da na samu,” in ji tsohon Sarkin Kano na 14.
“Dukkan wani shugaba na kasar nan ko duk wani shugaba na arewa a wannan lokacin bai kamata ya zauna cikin farin ciki ba saboda halin da mutanenmu suke ciki.
“Ko kai kana cikin tsaro, al’umma ba sa cikin tsaro. Idan kai ba ka cikin yunwa, al’umma na cikin yunwa. Kuma mutanen nan su ne mu.”
A cewar Sarki Sanusi kullum aka tuna halin da suke ciki dole ya zama ba a ji dadi ba.
“Don amanar da Allah ya dora mana ba za a mu iya dauka ba.”
Dangane da tattalin arziki kuwa, Sarki Sanusi ya ce duk matsalolin da Najeriya ke ciki a yau suna da dangantaka da matsalar tattalin arziki.
Ya ce matsaloli da suka hada da satar mutane don neman kudin fansa, da rikicin makiyaya da manoma da ta’addanci, da shaye-shaye da barace-barace duk suna da dangantaka mai karfi da tattalin arziki.
“Duk inda ka duba me yake kawo garkuwa da mutane? Me yake kawo fashi da makami? Me yake kawo rikici tsakanin makiyaya da manoma?
“Duk rigima ce kan tattalin arzikin kasa da halin rayuwa” in ji Halifan na Tijjaniyya.
Ya kara da cewa bai taba nadama kan duk wani mataki da ya dauka ba, kuma dama yana sane da cewa akwai abin da zai iya bayan duk wani mataki da ya dauka.
Ya ce ba ya tsoron bayyana duk wani ra’ayi da ya yi amanna cewa shi ne ra’ayi na gaskiya.