✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba wanda ya kawo wa Osinbajo cikas-Fadar Shugaban Kasa

Fadar Shugaban Kasa ta ce ba wanda ya yi kokarin tauye Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo lokacin da yake rike da mukamin mukaddashin shugaban kasa.…

Fadar Shugaban Kasa ta ce ba wanda ya yi kokarin tauye Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo lokacin da yake rike da mukamin mukaddashin shugaban kasa.
Babban Mai Taimaka wa Shugaban Kasa Na Musamman Kan Harkokin Yada Labari da Wayar da Kai, Garba Shehu ya ce Osinbajo a matsayinsa na mukaddashin shugaba kasa ya samu hadin kan ma’aikatan fadar shugaban kasa da kuma ’yan majalisar shugaban kasa.
Ya bayyana cewa ba don haka ba da bai samu nasara ba har ya samu yabo daga Shugaba Muhammdu Buhari.
Ya ce rahoton da ake yadawa cewa gungun ’yan bani-na-iya sun dawo don su dankwafar da Osinbajo tun dawowar Shugaba Buhari daga birnin Landan wani mataki ne na sake yada kalaman kiyayya don a dankwafar da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari.