✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ba na tsammanin INEC za ta yi adalci — Atiku

Har yanzu INEC ba ta gyara kurakuran da ta yi ba a zaben Shugaban Kasa.

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya ce ba ya tsammanin Hukumar Zabe ta Kasa INEC za ta yi adalci a zaben gwamnoni da na ’yan majalisar jihohi da ke gudana a kasar.

Atiku ya bayyana hakan ne a bayan ya kada kuri’arsa a rumfar zabe mai lamba 012 ta Unguwar Gwadabawa da ke Karamar Hukumar Jimeta a Jihar Adamawa.

Ya ce hukumar ba ta gyara kurakuran da ta yi a zaben Shugaban Kasa da ya gabata ba don haka ya karaya da yadda zaben ke gudanar sabanin yadda Dokar Zabe ta tanada.

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ya kirayi hukumar da ta gudanar da adalci sannan kuma ta karbi gyara.

Atiku dai yana kalubalantar nasarar Asiwaju Bola Tinubu na jam’iyyar wanda INEC ta ayyana a matsayin wanda ya lashe zaben Shugaban Kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.

%d bloggers like this: