✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba mu ƙara harajin VAT daga 7.5% ba —Ministan Kudi

Ministan Kuɗi, Wale Edun, ya ce babu gaskiya a labarin ƙara harajin VAT zuwa 10%

Ministan Kuɗin Najeriya, Wake Edun, ya ce har yanzu gwamnati ba ta ƙara ko sisi a kan abin take canza a matsayin harajin VAT ba.

Mista Wale Edun ya ce har yanzu VAT yana nan a kan 7.5% na farahsin kayan da harin ya shafa.

Ministan ya sanar da haka ne a safiyar Litinin, yana mai ƙaryata labarin da ke yawo cewa Gwamnatin Tarayya ta ƙara VAT daga 7.5% ya koma 10%.

Ya bayyana cewa har yanzu dokar harajin Najeriya ba ta yi gyara ko ƙari a kan 7.5% da aka saba karɓa ba a matsayin VAT.

“Har yanzu VAT na nan a 7.5%,  don haka, babu yadda gwamnati ko wata hukuma ko jami’inta su saɓa wa hakan,” in ji Wale Edun.

Ya ce a ƙoƙarin gwamnatin na samar da sauƙin haraji ne ma kwanan baya ta dakatar da karɓar harajin shigo da wasu kayayyaki daga waje.

“Ina nanata ce cewa, har yanzu 7.5% ne VAT a kan kayayyaki da hidimomin da wannan harajin ya shafa,” in ji sanarwar.