Ministan Tsaron Najeriya, Mohammed Badaru Abubakar ya musanta zargin da Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi cewa Gwamnatin Tarayya na kokarin yin sulhu da ’yan bindiga.
Hakan dai na cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin X (Twitter) na Ma’aikatar Tsaron Najeriya, a ranar Talata.
- Mun gaji da alkawuran yaudara – ’Yan ƙwadago ga Tinubu
- EFCC ta tsare masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba 80 a Kwara
Ministan ya ce Gwamnatin Tarayya ba ta umarci wani ko wasu su tattauna da ’yan bindiga a madadinta ba.
Sanarwar ta kara da cewa gwamnatin Tinubu na aiki domin ceto sauran daliban Jami’ar Tarayya da ke Gusau, a Jihar Zamfara, wadanda aka sace a ranar Juma’a.
A cewarsa, a yanzu haka sojoji sun ceto dalibai 13 da kuma leburori uku daga cikin wadanda maharan suka sace.
A ranar Litinin ne Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare ya fitar da wata sanarwa, inda ya yi zargin Gwamnatin Tarayya na yin tattaunawar sirri da ’yan ta’adda a jihar ba tare da sanin gwamnatin jihar ba.
Sai dai da yammacin Litinin, wata sanarwa daga ofishin Ministan Yada Labarai da Wayar da kan Jama’a, ta musanta batun, tare da zargin gwamnan na jihar da kokarin siyasantar da lamarin tsaro a Jiharsa.
Sai dai duk da haka gwamnan, ta hannun mai taimaka masa kan yada labarai, ya sake fitar da wata sanarwar a ranar Talata, inda ya ce gwamnatin jihar tana da shaidu kan tattaunawar da ke gudana tsakanin jami’an gwamnatin tarayya da ‘yan ta’addar.
Wannan zargi ya kawo rudani a tsakanin ‘yan Najeriya, inda mutane ke ganin ya fi dacewa gwamnatocin biyu su mayar da hankali kan ceto daliban jihar da aka sace.
Sai dai a ranar Litinin shugaba Tinubu ya bai wa jami’an tsaro umarni ceto daliban da ‘yan ta’addar suka sace.