Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta karyata rahotannin da ke cewa ta hana baki daga Najeriya shiga kasarta.
Ofishin Jakadancin UAE a Najeriya ya ce babu gaskiya a labarin sannan babu wata matsala a dangantakar da ke tsakanin kawayen biyu.
Sanarwar ofishin ta ta ranar Alhamis ta ce, “an samu raguwar masu zuwa ne saboda Najeriya ta dakatar da tafiye-tafiye zuwa kasashen waje.
“Amma Ofishin Jakadancin UAE da ke Abuja na aiki tare da Gwamnatin Najeriya domin ganin a koma tafiye-tafiye tsakanin kasashen biyu”, inji ofishin”.
Ta ce tun ranar 7 ga watan Yuli kasar ta bude iyakokinta bayan hana tafiye-tafiye a ranar 17 ga watan Maris domin takaita bazuwar cutar coronavirus.
Ta kara da cewa bayan samun saukin cutar kasar ta bayar da izinin shigogwar baki daga kasashen duniya ciki har da Najeriya.
“Amma da sharadin za su gabatar da shaidar gwajin da aka yi musu sa’a 92 kafin shigowarsu, da ke ke nuna ba su da cutar”.
Sanarwar ta bukaci jama’a su yi watsi da jita-jitar domin kasashen biyu na aiki tare domin kuma kawayen juna ne.