kabilar Ibo mazauna Jihar Bauchi sun ce babu ruwansu da yunkurin da wadansu tsirarri daga cikin kabilarsu ke yi na neman a raba kasar nan don kafa kasar Biyafara, inda suka ce babu wani abu cikin wannan magana illa neman ta da fitina.
Shugabannin kabilar Ibo jihar a karkashin jagorancin Rabaran Dominic Nkwocha ne suka bayyana haka lokacin da suka ziyarci Sakatariyar ’Yan jarida ta Jihar Bauchi.
Shugaban wanda Sakataren kungiyar Patrick Onuorah da sauran shugabannin Ibo suka rufa masa baya sun ce Najeriya kasa ce guda dunkulalliya da kundin tsarin mulki bai amince da irin wannan yunkuri ba, don haka su ba su goyon bayan yunkurin.
Shugabanin sun ce “A namu bangaren muna biyayya ga dokokin Najeriya, kuma mun yi imani Allah ne Ya hada mu mu yi rayuwa a wannan kasar Najeriya. Allah ne Ya so mu yi rayuwa cikin kasa daya. A bisa wannan dalilin ne muke barranta da kuma shelanta cewa ba mu tare da tsirari masu neman kafa kasar Biyafara kuma muna nesanta kanmu daga aikace-aikacensu.”
Sun nanata cewa za su ci gaba da mutunta doka da oda, kuma za su ci gaba yi wa dokokin kasa biyayya da mutunta al’ummar da suke zaune tare da su.
Sun gode wa Gwamnatin Jihar Bauchi kan yadda take kokarin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jihar kuma sun shawarci ’yan kabilar Ibo da suke zaune a jihohin Arewa maso Gabas su ci gaba da kwantar da hankalinsu domin gwamnonin jihohin da jami’an tsaro sun yi musu alkawarin kare lafiyarsu da dukiyoyinsu.