Shugaban Majalisar Malamai ta Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta Kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya ce, bai amince da matakin da aka dauka na dakatar da Na’ibin Kwamishinan ’Yan sanda (DCP) Abba Kyari ba.
Sheikh Sani Yahya Jingir, ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da wa’azi, a Masallacin Juma’a na ’Yan Taya da ke garin Jos.
- Mutanen da za su wakilci Buhari a auren dansa Yusuf a Bichi
- ‘A daki daya muke kwana da Sarkin Kano Sanusi II’
Ya ce shi ya yarda da Abba Kyari, domin jajirtatcen dan sanda ne da yake gudanar aikinsa dare da rana.
Ya ce, “Wallahi akwai barayi ’yan Najeriya da aka kama, sun saci biliyoyin Naira, amma suna nan suna yawo.
“Tsakani da Allah duk masu zargin Abba Kyari, babu wanda ya ce ya yi sata, an kama shi.
“Zargin da ake yi masa, shi ne wai ya taba hira da wani xan damfara, wannan ba sata ba ce. A kan wannan ne za a ce an dakatar shi daga aikinsa?’’
Ya ce abin takaici ne a ce gwamnoni da ’yan majalisa da malamai, suna ji amma sun yi shiru, kan wannan al’amari ba tare da sun yi magana ba.
Ya ce, “Ni Sani Yahya Jingir ban yarda a dakatar da Abba Kyari ba. Don an ga Shugaban Kasa Buhari ya yi tafiya ce aka yi wannan abu.
“A kullum idan Buhari ya yi tafiya, sai an cuce mu a Najeriya. Don Allah ’yan majalisa da gwamnoni ku yi magana kan wannan al’amari.”