✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda Iyan Zazzau ya rasu

Hakikanin yadda Alhaji Bashar Aminu ya rasu daga bakin dansa

Iyalan marigayi Iyan Zazzau, Alhaji Bashar Aminu sun karyata jita-jitar da ake yadawa cewa akwai hannun wani bil Adama a mutuwar marigayin wanda ya rasu a ranar Juma’a.

Rahotanni sun bayyana cewa ana yada jita-jitar cewa kashe marigayin aka yi saboda kalubalantar nadin da aka yi wa Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau na 19 a gaban kotu.

Aminiya ta ruwaito cewa, Alhaji Bashar Aminu ya rasu ne ranar Juma’a a Jihar Legas, inda a ranar Asabar aka kawo gawarsa Zariya aka gudanar da jana’izarsa tare da sanya gawarsa a makwanci a gidansa da ke Unguwar Sabon Gari a Zariya.

Bayan wani lokaci kankani da labarin mutuwarsa ya karade Jihar Kaduna a ranar Juma’a, jita-jita ta fara tashi cewa kashe shi aka yi a Legas yayin da ya fito daga gidansa zuwa masallaci domin Sallar Asuba.

Sai dai a yayin tattaunawa da Aminiya bayan an kammala jana’iza, Shehu Iya Sa’idu, wanda ke rike da rawanin Tafidan Dawakin Zazzau wanda kuma tamkar dan da marigayin ya haifa ne, ya ce jita-jitar uban rikon nasa ba ta da wani asali ballanta tushe.

Ya ce kasancewarsa mutumin da ya fi kusanci ga marigayin, yana da tabbacin cewa mutuwa ce ta zo masa daga Allah ba tare da sanadin wani bil Adama ba.

A cewarsa, “Dama ya kasance yana fama da rashin lafiya amma saboda kasancewarsa jarumi ya ci gaba da jajircewa kuma mutane da dama ba su da masaniya a kan hakan sai dai na jikinsa.

“Jita-jitar cewa harbin shi aka yi ba gaskiya ba ne, kuma ina daya daga cikin mutane mafiya kusanci da shi saboda ya kasance tamkar mahaifi a gareni domin kuwa tun ina dan shekara biyu yake rike da ni.

“Saboda haka ina mai tabbatar muku da cewa lokacinsa ne ya yi, kuma Allah wanda Ya ba mu shi Ya karbi abinSa wanda a yanzu babu abin da muke rokon face Ya jikan sa da rahama kuma Ya sa Aljanna Firdausi ce makomarsa,” kamar yadda ya shaida wa Aminiya

Alhaji Sa’idu ya ce an dawo da gawar marigayin ne zuwa cibiyarsa domin kafin rasuwarsa ya bayar da wasiyyar cewa a tabbata an sallaci gawarsa a Masallacin Juma’a na Sabon Gari da ke Zariya kuma an binne shi a nan.

Ya ce “muna yi wa Allah Madaukakin Sarki godiya da ya ba mu ikon sauke wannan nauyi na wasiyya da bayar.”

%d bloggers like this: