Rundunar ‘yan sandan Jihar Imo, ta ce jami’anta ba kama Shugaban Kungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC), Joe Ajaero suka yi ba a Owerri, babban birnin jihar.
A ranar Laraba ne shugaban yada labarai na NLC, Benson Upah, ya ce jami’an ‘yan sanda dauke da makamai sun yi awon gaba da Ajaero a sakatariyar NLC da ke Imo.
- Majalisa ta tabbatar da Chira a matsayin babban mai binciken kudi na tarayya
- Kotu ta kori Gabriel Suswam a matsayin Sanatan Benuwe
Ya ce “’Yan sanda dauke da makamai sun yi awon gaba da shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya, Kwamared Joe Ajaero, mintuna kadan da suka gabata daga sakatariyar NLC a Owerri, sun tafi da shi wurin da ba mu sani ba,” in ji Upah.
Da yake mayar da martani kan lamarin, Henry Okoye, kakakin rundunar ‘yan sandan Imo, ya ce shugaban NLC ya yi sa’insa da wasu mutane a filin jirgin saman jihar.
Okoye ya ce yunƙurin daukar mataki ne ya sanya ‘yan sanda suka tsare shugaban NLC a hedikwatar ‘yan sandan jihar don ba shi kariya.
“Bayan samun wannan rahoto, rundunar ‘yan sandan Imo ta gaggauta tura jami’an ‘yan sanda zuwa wurin tare da kai wa shugaban NLC dauki zuwa hedikwatar ‘yan sanda ta jihar domin tabbatar da tsaron rayuwarsa,” in ji kakakin ‘yan sandan.
“Bayan haka kwamishinan ‘yan sanda ya ba da umarnin a kai shi sashen kula da lafiya na ‘yan sanda da ke Owerri, inda za a kula da lafiyarsa sakamakon shirin kai masa harin.
“Don haka an ba shi cikakkiyar kariya da tsaro don ci gaba da sauran ayyukansa na yau da kullum.”
A ranar 30 ga watan Oktoba, ne NLC ta yi alkawarin za ta dakatar da ayyuka a Imo daga ranar 1 ga watan Nuwamba, domin bayyana rashin jin daɗinta kan take hakkin ma’aikata.
Ajaero ya yi zargin cewa gwamnatin Imo ba ta biya wasu ma’aikata albashi na tsawon wata 20 ba.