Wani jigo a jam’iyyar adawa ta PDP kuma tsohon Sanatan da ya wakilci mazabar Edo ta Kudu a Majalisar Dattijai, Roland Stephen Owie, ya ce in ba don tsarin karba-karba ba, yankin Arewacin Najeriya zai iya shekara 300 yana mulkin Najeriya.
Ya kuma gargadi jam’iyyarsu ta PDP da ta kai kujerar takarar Shugabancin Kasarta a 2023 zuwa Arewa, muddin tana son ta lashe zaben da ke tafe.
- Zaben Anambra: Jami’in INEC ya tsere da takardun sakamakon zabe guda 42
- Likitoci sun sa wa mutum kodar alade a Amurka
Sanata Roland, wanda ya taba zama Bulaliyar Majalisar Dattijai a 1999, ya bayyana hakan ne a cikin wata tattauanwarsa da jaridar Daily Trust, lokacin da yake tsokaci akan inda ya fi kamata a kai kujerar takarar a zabe mai zuwa.
A cewarsa, “Shi fa zabe magana ce ta yawan kuri’u, ka duba adadin mutanen da suka yi rijistar zabe a Najeriya, za ka ga yawan na kowacce yanki. Matukar ba ka da yawan kuri’u, to babu inda za ka je.
“Idan saboda son kai muka yi watsi da tsarin karba-karba, to ina mai tabbatar maka sai an shekara 300 Kudancin Najeriya bai shugabanci kasar nan ba.
“Za a sami zaman lafiya ne kawai in aka kwatanta adalci, a zahirin gaskiya ma babu tsarin karba-karba a Kundin Tsarin Mulkin PDP, amma an kawo shi ne don a sami maslaha, dalilin kenan ma da ya sa aka kawo Olusegun Obasanjo a 1999 don a danne kirjin Yarabawa saboda soke zaben Abiola da aka yi na 12 ga watan Yuni.
“Idan ka lissafa sosai, za ka ga cewa daga 1999 zuwa yau a karkashin mulkin PDP, yankin Kudu ya yi shekara 13 yana mulki, yayin da Arewa ya yi shekara uku kacal. Muddin PDP ta dauki takara a 2023 ta kai Kudu, to ta yi rashi adalci.
“PDP ce kadai jam’iyyar da ta yi amanna da hadin kan kasar nan, ya kamata kuwa ta kai takara Arewa a 2023.
“Amma a APC kuwa, tun da Arewa ta yi shekara takwas, babu laifi in sun kai takararsu Kudu,” inji Sanata Roland.