✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ba da yawuna Buhari zai kara mulki ba —Lawan

Wa’adi biyu doka ta bayar, ba za yarda a yi gyaran kundin tsarin mulki ba

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya karyata sakon Twitter da ke yawo cewa zai so a gyaran kundin tsarin mulki don kara wa Shugaba Muhammadu Buhari damar zama a mulki bayan 2023 idan Buharin yana so.

Lawan ta bakin kakakinsa, Ola Awoniyi, ya ce bai taba yin wannan furucin ba ko kafin zaben 2019, don haka ya bukaci jama’a da su yi watsi da sakon.

Ya ce yana kan abin da dokar kasa ta tanadar na wa’adi mulki biyu ga Shugaban Kasa, kuma ba zai goyi bayan duk wani abu sabanin haka ba.

“Matsayin kundin tsarin mulkin Najeriya a fayyace yake game da wa’adin mulkin Shugaban Kasa, wanda shi ne ra’ayin galibin ’yan Najeriya.

“Sashe ne 137(1)b ya tanadi cewa: Mutun na iya cancantar a zabe shi ya zama Shugaban Kasa (b) A zabe shi har sau biyu a ofishin.

“Shugaban Majalisar Dattawa bai taba ganin kuskure a cikin abin da wannan sashe ya tanada ba.

“Lawan dan Majalisar Tarayya ne a 2006 lokacin da ta yi fatali da yunkurin tsawaita wa’adin mulkin Shugaban Kasa.

“Abin da Majalisar ta yi a wancan lokaci shi ne daidai da ra’ayin ’yan Najeriya.

“Saboda haka ba yadda za a yi yanzu ya koma goyon bayan irin wancan yunkuri.

“Ya fahimta kuma yana tare da kundin tsarin mulki kai da fata kuma ba zai taba goyon bayan yunkurin sauya shi ba,” inji sanarwar.