Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, ta musanta rahoton sace matafiya a kan titin Kaduna zuwa Abuja.
Wannan na cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, ASP Mansir Hassan ya fitar a ranar Talata.
- ’Yan bindiga na neman N50m kudin fansar hakimin Abuja
- DAGA LARABA: Matsalolin Da Suka Kewaye Kannywood
“Muna son tabbatar da cewar ba sace kowa a hanyar Abuja zuwa Kaduna ba; an dai yi artabu tsakanin jami’an tsaro da ’yan bindiga a kan hanyan a ranar 6 ga watan Janairu da misalin karfe 11:30 na dare.
“Al’amarin ya faru ne a lokacin da yyan bindiga suka yi yunkurin tsallaka babbar hanyar da ke yankin Dogon Fili da ke kan hanyar kauyen Jere.
“Amma rundunar ’yan sanda ta fatattake su da ruwan harsasai, inda suka tsere da raunin harbin bindiga,” in ji shi.
Hassan ya ce batun sace matafiya a kan titin babu kamshin gaskiya a cikinsa, domin kuwa babu wanda aka sace.
Sai dai ya bukaci al’ummar yankin da su zama masu sanya ido tare da kai rahoton duk wani motsi da ba su yarda da shi ba ga jami’an tsaro mafi kusa da su.
Kazalika, ya ce kwamishinan ’yan sandan jihar, Ali Dabigi, ya bukaci ’yan jarida da su rika tantance labarai da hukumomin tsaro da abin ya shafa kafin su yada.