✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga na neman N50m kudin fansar hakimin Abuja

Maharan sun dage kan dole sai iyalan hakimin sun biya miliyan 50 a matsayin kudin fansa.

’Yan bindigar da suka yi garkuwa da hakimin Pandan-Gwari tare da wasu mutum biyar a unguwar Kawu da ke Karamar Hukumar Bwari sun bukaci Naira miliyan 50 kafin sako su.

Aminiya ta ruwaito cewa a ranar 26 ga watan Disamba, 2023 ’yan bindigar suka kai hari fadar hakimin suka yi awon gaba da shi tare da mutanensa biyar.

Wata majiya daga iyalan hakimin, wacce ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa Aminiya a ranar Talata cewa, shugaban ’yan bindigar ya bukaci a biya su kudin fansa Naira miliyan 50.

Ya ce tattaunawar da aka yi game da kudin fansar ta faru ne tsakanin daya daga cikin iyalan hakimin, wanda yake ta rokon ’yan bindigar kan su rage kudin fansar amma sun ki.

“Ina jin magana ta karshe da mutumin ya yi da shugaban ’yan bindigar a ranar Juma’a, inda shi kuma ya dage kan sai an biya su Naira miliyan 50, kuma tun daga wannan lokacin ba su sake kira ba,” in ji shi.