Fadar Shugaban Kasa ta mayar da martani kan ra’ayin jaridar Daily Trust da aka wallafa ranar Lahadi kan matsalar tsaro da yawan kashe-kashe a Najeriya.
A cikin rubutun, mai taken ‘Rayuwa ba ta da wata daraja a gwamnatin Buhari ta Najeriya’, wanda ya karade gari kuma ya jawo cece-kuce matuka, jaridar ta kawo misalan kashe-kashen da ake fuskanta a kasar nan, musamman ma a yankin Arewa.
- Najeriya A Yau: Me Dimokuradiyya Ta Tanada Wa Talaka Idan Tura Ta Kai Bango?
- Matsalar tsaro: JNI ta bukaci Musulmi su dukufa addu’o’i na musamman
Daga kone fasinjoji 42 da ransu a cikin mota a Sakkwato, zuwa kisan Kwamishina a Katsina da kuma kisan masallata a Neja, jaridar ta zargi gwamnatin da rashin yin wani katabus wajen kawo karshen matsalar.
Dubban mutane ne dai, musamman a kafafen sada zumunta na zamani, suka yi ta tsokaci a kai, inda suke Allah wadai da gwamnatin.
To sai dai a cikin wata sanarwa da mai taimaka wa Shugaban Kasa kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu ya fitar da maraicen Lahadi, fadar ta amince cewa jaridar ta lalubo matsalar tun daga tushe.
Sai dai ta ce ba a iya Najeriya ne kawai ake fuskantar irin wadannan kalubalen ba, inda ta ce tana iyakar kokarinta wajen ganin bayan matsalar.
“Ya zama wajibi mu mayar da martani la’akari da girman batun da Daily Trust ta tattauna.
“Ci gaba da tashin hankali da zubar da jini a Arewa da ma Najeriya ba abu ne da za a lamunta ba. Babu wanda yake tababa akan girman matsalar, tun ma ba ga Shugaban Kasa ba.
“Kullum sai Buhari ya yi wa wadannan mutanen da iyalansu addu’a, kuma abu mafi muhimmanci, yana kara jaddada cewa kawo karshen ayyukan ta’addanci shi ne babban abin da ya sa gaba,” inji sanarwar.
Daga nan sai fadar ta ce tana yin dukkan mai yiwuwa wajen kawo karshen matsalar, musamman ta hanyar dakile hanyoyin samun kudaden shigarsu da ma wasu matakan.
Sanarwar ta ce tana da kwarin gwiwar cewa nan ba da jimawa ba matsalar tsaro za ta zama tarihi a Najeriya.