✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ba a ga watan Sallah ba a Saudiyya

Hakan dai na nufin sai ranar Litinin za a yi Sallah a kasar

Saudiyya ta tabbatar da cewa ba ta ga watan Shawwal ba a ranar Asabar, wanda hakan ke nuni da cewa bana azumi 30 za a yi a kasar, Sallah kuma sai ranar Litinin mai zuwa.

Hakan dai ya biyo bayan rashin ganin watan a sassa daban-daban na kasar a ranar Asabar.

A wani sako da suka wallafa a shafin masallatan Harami a dandalin sada zumunta na Facebook mai suna Haramain Sharifain a ranar Asabar, hukumomin Sauddiyyar sun ce za a cika azumi 30 a bana, kuma bikin Karamar Sallah sai ranar Litinin mai zuwa.

Ko a bara ma dai azumi 30 aka yi a kasar sakamakon rashin ganin jinjirin watan ranar 29 ga watan na Ramadan.

Musulmai a fadin duniya dai na yin bukukuwan Karamar Sallah ne bayan kammala wata daya suna azumtar watan Ramadan.