Hukumar Kula da Ganin Wata ta kasar Saudiyya ta sanar da cewa ba a ga jinjirin watan Shawwal ba a kasar.
Hakan na nufin za a azumci ranar Laraba inda Ramadanan bana za a cike ya zama an yi azumi 30 kenan.
- Shin an sake nada Sarki Sanusi Khalifan Tijjaniyya?
- An hana zuwa Filin Idi a Abuja —Minista
- An yi fashi a kusa da Fadar Shugaban Kasa
- An kama ’yan Boko Haram 13 a Kano
Don haka ranar Alhamis, 13 ga watan Mayu, 2021 ce za ta yi daidai da 1 ga watan Shawwal na shekarar 1442 Hijiriyya.
Akan haka ne Hukumar gudanarwar kasar Saudiyya ta umarci jama’ar kasar da su cike azuminsu zuwa 30, sannan su yi idi a ranar Alhamis ta jibi.
Tun a ranar Litinin ce dai wasu masana Ilimin Taurari da Sararin Samaniya suka yi hasashen cewar ba za a ga jinjirin watan Shawwal ba a ranar Talata, har sai zuwa ranar Laraba.