Hanyoyin yin kyauta da kyautatawa:
Ciyar da mai azumi:
An karbo daga Zaidu bin Khalid Al-Juhni ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wanda ya ciyar da mai azumi yana da lada gwargwadon ladarsa (mai azumin) ba tare da an rage wani abu daga ladan mai azumin ba.” (Tirmizi, Hadisi na 807 da Ibnu Majah, Hadisi na 1746, kuma Tirmizi ya ce: “Wannan Hadisi ne mai kyau ingantacce).
Kyautata wa iyaye da sadar da zumunta:
An karbo daga Abu Huraira (RA) ya ce: “Wani mutum ya zo wurin Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wane ne mafi hakkin mutane ga in kyautata zamana da shi?” Sai ya ce: “Mahaifiyarka.” Ya ce, “Sai kuma wa?” Ya ce: “Sa’annan mahaifiyarka.” Sa’annan ya ce: “Sai kuma wa?” Ya ce, “Mahaifiyarka.” Ya ce, “Sai kuma wa?” Ya ce, “Sa’annan mahaifinka.” (Buhari Hadisi na 5971 da Muslim Hadisi na 2548).
Anas bin Malik ya ce: “Na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Wanda yake son a yalwata masa arzikinsa ko bayansa ya yi albarka, to ya sadar da zumuntarsa.” (Buhari Hadisi na 5985 da Muslim Hadisi na 2557).
Adda’u ya ce: “Dirhamin da na bayar da shi ga dangina ya fi min dadi daga Dirhami dubu da na ciyar da waninsu. Sai wani ya ce masa: “Ya Abu Muhammad koda dangina sun kai ni wadata?” Ya ce: “Koda sun fi ka wadata.” (Mukarimul Akhalak na Ibnu Abu ad-Duniya, shafi na 62).
3. Sadaka da ciyarwa da sauran ayyukan alheri:
An karbo daga Abu Huraira (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Kowane sulhu daga mutane akwai sadaka a kansa. Kowane yinin da rana ta fito a cikinsa idan ka yi adalci a tsakanin mutum biyu sadaka ce. Ka taimaki mutum a kan dabbarsa ka dora shi a kanta ko ka dora masa kayansa a kanta sadaka ce. Kalma mai kyau sadaka ce, kuma kowane taku da kake yi zuwa Sallah sadaka ce, kuma ka dauke abin cutarwa daga kan hanya sadaka ce.” Buhari da Muslim suka ruwaito. Annawawi ya ce, “Malamai sun ce: “Abin da ake nufi: Sadaka a nan babin kwadaitarwa ce, ba ta wajibci da lizimtarwa ba.” (Sharhu Muslim, 7/95).
4. Ramadan watan Alkur’ani da tsayuwar dare:
Alkur’ani da watan Ramadan
Allah Madaukaki Ya ce: “Watan Ramadan ne wanda aka saukar da Alkur’ani a cikinsa yana shiriya ga mutane da hujjoji bayyanannu daga shiriya da rarrabewa.” k:2:185).
An karbo daga Ibnu Abbas (RA) ya ce: “An saukar da Alkur’ani dukkansa a dunkule lokaci guda zuwa saman duniya a daren Lailatul kadari cikin watan Ramadan, sai ya kasance idan Allah Ya yi nufin wani abu ya faru a duniya sai Ya saukar da shi daga gare shi, har Ya gama tara shi.” Ibnu Jarir Addabari ya fitar da shi a cikin Tafsirinsa mujalladi na 2 shafi na 145 da isnadi ingantacce. Kuma daga gare shi ya ce: “Manzon Allah ya kasance mafi kyauta da alheri a tsakanin mutane, kuma ya kasance ya fi yin kyauta a cikin watan Ramadan, lokacin da Jibrila ke ganawa da shi. Ya kasance yana ganawa da shi a kowane dare na Ramadan, sai su yi darasun Alkur’ani. Kuma Manzon Allah (SAW) wajen yin kyauta ya fi iskar sarfa.” Buhari da Muslim suka ruwaito.
Annawawi ya ce: “Abin da za a amfana daga wannan Hadisi na hukunce-hukunce shi ne: An so mudarasar Alkur’ani a wannan wata mai albarka.” (Sharhu Sahihil Muslim, 15/69).
Ibnu Hajrin kuma ya ce: “Daga cikin fa’idojin da za a cirato daga Hadisin akwai: Girmama watan Ramadan ta hanyar kebance shi da fara saukar Alkur’ani a cikinsa, sai kuma sake bijiro da karatun abin da ya sauka daga gare shi. Hakan ya hada da yawan saukar Jibrilu (AS) a cikinsa, kuma a cikin yawan saukarsa akwai karuwar alheri da albarka marar kidayuwa. Kuma wata fa’idar ita ce: Lallai falalar lokaci na samuwa ne sakamakon karuwar ayyukan ibada, kuma akwai cewa yawaita tilawa na haifar da karuwar alheri. Kuma a cikinsa an so yawaita ibada a karshen rayuwa da muzakirar alheri da ilimi, domin ba boyayye ba ne karuwar tunatarwa da wa’azantarwa a cikinsa. Kuma a cikinsa akwai dalilin cewa, lallai daren Ramadan ya fi yininsa, kuma abin da ake nufi da tilawa shi ne halarto da zuciya da fahimta yayin karatu, kuma ana zaton hakan ya fi samuwa a cikin dare, saboda abin da ke cikin yini na shagulgula da bijirowar ababen duniya.” (Fathul Bari, 9/45).
Wannan ya sanya magabatan kwarai suke tashi tsaye wajen tilawar Alkur’ani, misali Ibrahim An-Nakha’i ya ce, “Al-Aswad yana sauke Alkur’ani a kowane dare biyu na Ramadan, inda yake barci a tsakanin Magariba da Isha’i kawai, kuma yana sauke Alkur’ani a dare shida na sauran watanni.” (Siyar A’alamin Nubla’i, 4/51).
Azumi da abubuwan da yake koyarwa (03)
Hanyoyin yin kyauta da kyautatawa: Ciyar da mai azumi: An karbo daga Zaidu bin Khalid Al-Juhni ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wanda ya…