Makon jiya mun tsaya ne daidai inda muka yi karatu game da maganar da muka soma yin bincike a kai wato:
Neman Fuskar Ubangiji Allah Domin Cika AlkawarinSa: A cikin Littafin Daniel 9: 2 – 3, maganar Allah na cewa, “A cikin shekara ta fari ta mulkinsa, ni Daniel ta wurin littattafai na gane lissafin yawan shekaru, wadanda maganar Ubangiji ta ambace su ga Annabi Irmiya, kafin risbewar Urushalimata cika, shekara saba’in ke nan. Na kuwa kafa fuskata zuwa wajen Ubangiji Allah, domin in yi bida gare Shi ta wurin addu’o’i da roke-roke tare da azumi da tsummoki da toka.” ’Ya’yan Isra’ila sun yi ta aikata abin da Allah Ya umurce su su yi, amma sun ki su yi biyayya ga sharuddan Allah, Allah, ta wurin bawanSa Annabi Irmiya ya kawo musu gargadi su yi hankali da rayuwarsu; su dawo ga bin tafarkin Allah, amma duk da haka su ka ki ji; sai Allah Ya ce musu, idan ba ku bar aikata zunubi ba, Ni zan bar magabtanku su zo su ci nasara a bisanku, su kuma dauke ku ganima ku zama bayi kuna yi musu bauta a kasarsu wato Babila. Suna gani kamar ba da gaske ne Allah zai bar magabta su ci nasara a kansu ba, suka ci gaba da aikata zunubinsu. Rana daya Allah sai Ya janye kariyar da yake yi musu, Nebucadnezar babban Sarkin kasar Babila ya auko wa kasar Isra’ila da yaki; ya kuma ci nasara, haka nan ya kwashe su zuwa kasar Babila suka zama bayi ga mutanen Babila. A lokacin da suka tafi kasar bauta, shi Daniel mai kimanin shekara goma sha bakwai ne kawai.
Abu daya wanda shi Daniel bai daina yi ba, shi ne yin binciken maganar Allah da kuma yin addu’a domin ya san mene ne shirin Allah domin rayuwarsu a cikin kasar bauta, a haka nan ne ya gane cewa za su yi shekara saba’in a kasar bauta kafin su dawo kasarsu ta gado. A haka din ne ya shiga yin azumi domin Ubangiji Allah Ya ba shi bayanin abin da zai faru da su. Ina so mu gane wannan asirin duk lokacin da al’ummar kasa suka shiga mawuyacin hali, akwai abin da za mu iya yi domin mu samu taimakon Allah; Yin azumi. Sau da dama mukan manta da wannan sashin rayuwa, haka nan sai mu bar hanyar da za mu samu taimako daga wurin Ubangiji Allah. Mu sake inda muka yi a cikin Littafin Timothawus ta fari sura biyu aya daya zuwa hudu wadda take cewa “A farko dai ina umurni a yi bide-bide da addu’o’i da roke-roke da godiya, saboda da dukkan mutane; domin sarakuna da dukkan wadanda ke cikin matsayin manya; domin mu yi ranmu mai natsuwa da hankali kwance cikin dukkan ibada da kimtsa fuska. Wannan mai kyau ne, abin karba kuwa ga Allah Mai cetonmu; shi wanda yake nufi dukkan mutane su tsira, kuma su kawo ga sanin gaskiya.” Kamar yadda Daniel ya yi azumi da addu’a domin ya nemi nufin Allah game da mutanen, haka nan za mu iya yin azumi domin wadansu al’umma da suke cikin damuwa ko kuwa kalubale da ya fi karfinsu. Sau da dama muna gani kamar damuwar wasu ba lallai tamu ba ce.
A wannan kasa tamu lokaci ya zo daidai da za mu nemi nufin Allah game da zaben da ake so a yi a shekara mai zuwa. Kada mu yi sakaci muna tsammani akwai lokaci, za mu iske kanmu cikin wahala idan ba mu tashi mun magance wannan yanzu ba. Hanyar magance ta kuwa neman fuskar Ubangiji ne cikin addu’a da azumi. ’Yan siyasarmu da dama ba su da lokacin da za su kebe domin rokon Allah Ya bishe su cikin dukkan abin da suke so su yi, abin da suka sa a gaba shi ne su ci nasarar zabe. ’Yan uwana! Wannan lokacin yana da muhimmanci kwarai ga mai son zaman lafiya a wannan kasa. Idan da ma ba ka soma ba, sai ka soma yin azumi da addu’a kamar yadda Allah zai bishe domin Shi Ubangiji Allah Masanin abu duka ne domin Ya zaba mana mutane nagari masu tsoronSa Ya sa su bisa ragamar mulkin wannan kasa, kada mu yi sakaci.
Domin tuba ta gaskiya – wato neman Ubangiji Allah da jinkanSa:
Za mu yi karatu kadan daga cikin Littafi Mai tsarki – Joel 2 : 12 – 17, Maganar Allah na cewa “Amma ko yanzu, inji Ubangiji, ku juyo miNi da dukan zuciyarku, tare da azumi da kuka da bakin ciki: ku tsaga zukatanku ba tufafinku ba, ku juyo wurin Ubangiji Allahnku: gama Shi Mai alheri ne cike da juyayi, Mai jinkirin fushi, Mai yalwar jinkai, Yana sake nufinSa a kan masifar da Ya shirya. Wa ya sani ko ba za Ya juyo Ya sake nufinSa ba, Ya bar albarka a bayanSa, wato hadaya tagari da ta sha ga Ubangiji Allahnku? A busa kaho cikin Sihiyona, a tsarkake kwanakin azumi, a tattara taro mai saduda, a tara mutane, a tsarkake jama’a, a tattara dattawa, a tattara yara da wadanda ke shan nono: bari ango ya fita daga dakinsa, amarya kuma daga cikin lollokinta.
Bari Priest da masu hidimar Ubangiji, su yi kuka tsakanin haraba da bagadi, su ce, Ka kebe jama’arKa, ya Ubangiji, kada Ka ba da gadonKa zuwa zargi, har da al’ummai za su mallake su: don mene ne a cikin dangogin mutane za su ce, ina Allahnsu?” A cikin Littafin Zabura 109 : 22 – 26 , maganar Allah tana cewa “ Gama mai talauci ne ni, mai mayata, an rotsa zuciyata kuma daga cikina, Na shude kamar inuwa sa’adda ta mike, an faffaure ni kamar fara, Guwayuna sun yi gyadu-gyadu domin azumi, jikina kuma duk ya kasa kiba. Na zama abin zargi a wurinsu: Sa’adda sun gan ni sukan kada kansu. Ka taimake ni ya Ubangiji Allahna, Ka cece ni bisa ga jinkanKa.” Nehemiah 1: 3 – 4, tana cewa “Suka ce mini, Ringin da sun wanzu daga bauta a can cikin yankin kasa, suna cikin wahala da shan zargi ainun: ganuwar Urushalima ta rushe, kofofinta kuma sun ci wuta. Ya zama fa, sa’adda na ji wadannan zantuka, sai na zauna na yi kuka, na yi ’yan kwanaki ina bakin ciki, na yi azumi da addu’a a gaban Allah na sama.” Za mu dasa aya a nan domin mu samu sararin yin koyarwa mako na gaba idan Allah Ya yarda. Kada mu manta da neman nufin Allah musamman a wannan lokaci da muke ciki na kokarin yin zaben sababbin shugabanni a wannan kasa. Allah Ya sa mu dace, amin.