✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Azumi (12)

Makon da ta shige, muna magana ne game da amfanin yin azumi ga mai bin Yesu Kristi, mun ga yadda addu’ar mu za ta sami…

Makon da ta shige, muna magana ne game da amfanin yin azumi ga mai bin Yesu Kristi, mun ga yadda addu’ar mu za ta sami karbuwa da samari a gaban Ubangiji Allah idan har mun hada da azumi. Allah da kansa ya ce za ku kira, Ubangiji ko za ya amsa,  A yau dai ina so mu kawo ga karshe wannan koyarwar  mu a kan Azumi
    UBANGIJI KUMA ZA YA JA MAKA HANYA:-  Babu wani abin da ya fi dadi fiye da sanin cewa Allah da kansa ne ka ja mana gora,  mutum kamar makaho ne, wanda bai san inda zai sa kafarsa ba, bai san abin da zai yi karo da shi ba, bai san irin hadarin da ke gabansa ba, idan ba shi da wani wanda zai ja masa gora; hakanan mutum yake, ba mu san inda muka dosa ba cikin rayuwarmu na yau da kullum, idan har mun ci gaba haka kuwa, to babu shakka za mu fada cikin ramin wahala, amma idan muka yarda mu bar Ubangiji Allah ya yi mana jagora, to debe shakka za mu sami chikakken tsarewa daga kowache irin hatsari na rayuwar yau da kullum. Allah da kansa zai tsare mu daga dukan magabta, hakannan za mu sami huta a cikin Yesu Kristi. A cikin aya 11 nan maganar Allah na koyasda mu da chewa “Ubangiji kuma za ya ja maka hanya tuttur, ya kosar da ranka cikin kekasassun  wurare,  ya karfafa kasusuwanka, za ka zama kamar lambu wanda an yi masa ban ruwa, mabulbulan ruwa kuma, wadda ruwnta ba shi karewa ba”. Ishaya 58 : 11. Irin wannan yanayi ma abin farin ciki ne, idan ka shiga lambu ko kuwa gonar da take da cikakken ban ruwa,  har ciyawar da take cikin gonar  ma ta na jin dadi. Yawancin lokaci muka manta da irin wannan alherin, domin mun ki mu sa kai cikin irin wannan rayuwa ta ibada. Masu bin Yesu Kristi da dama ba su dauki yin azumi kamar wani abu mai muhimmanci ba ne, su na gani kamar ko ba su yi azumi ba, za su samu dukan biyan bukatunsu, gaskiyar kuwa ita ce, akwai wadansu abubuwa wadanda ba za mu taba samu ba, sai ta wurin yin addu’a da azumi.  
Ina so mu kawo ga karshe wannan koyarwa a yau! Muna cikin mawuyacin hali a wannan loto cikin wannan kasa tamu, dukan masu bin Yesu Kristi mu tuna muna da aiki wadda Allah ya sa a hannun mu, wannan aikin kuwa shi ne yin addu’a ga Allah Ubangijin mu, domin wannan kasa da kuma shugabaninta, Mulki daga wurin Allah ne, duk wanda ya hau bisa ragamar mulki, mu sani Allah ne ya ba shi, ko kuwa ya ba ta; a cikin Litafin Romawa 13 : 1 – 5 maganar Allah na cewa: “Bari kowane mai rai shi yi zaman biyayya da ikon masu mulki: gama babu wani iko sai na Allah; ikokin da ke akwai kuma sanyayyu ne na Allah. Wanda ya yi jayayya da iko fa, yana jayayya da umurnin Allah ke nan, masu jayayya kuwa za su jawo wa kansu hukunci. Gama masu mulki ba abin tsoro ba ne ga masu aikin nagarta, sai ga na mugunta. Kana so ka zamna da ikon fa,  sai ka yi abin da ke nagari, za ka samu yabo kuwa daga gareshi: gama shi mai hidimar Allah a gareka zuwa nagarta. Amma idan kana aikata mugunta, to ji tsoro; gama ba kawai ya ka rike da takobi ba: gama mai hidimar Allah ne, mai ramawa da fushi ne a kan mai aikata mugunta. Domin wannan fa ya wajaba gareku ku yi zaman biyayya, ba domin fushi kadai ba, amma sabili da lamiri kuma”. Ina so mu gane wannan sosai : Allah shi ya ke yarda ya ba da mulki ga duk shi wanda ya dace; Allah kadai ke da ikon ta da matalauci daga cikin  halin kaskanci, ya kuma hau da shi bisa kursiyin sarauta, mulki daga gareshi yake,  kowane mutum mai gaba da mulkin da Allah ya sa ko kuwa ya kafa, yana gaba ne da nufin Allah. Gaskiya muna lokacin siyasa, mutane sun fita neman zabe domin su hau ragamar mulki a wannan kasa,  yawancin lokaci abu gida daya wadda a kan manta a yi shi ne neman nufin Allah cikin duk abin da mu ke yi. Ko da shi ke mu na ce da kanmu mu masu ibada ce gaskiyar ita ce mukan manta mu nemi nufin Allah cikin siyasar da muke yi. Idan muka kasa kunne ga irin kalaman da suke fitowa daga bakin mutane, domin su na so a zabi nasu; sai ka yi mamakin inda muke dosa a zaman muna ’yan kasa. Mene ne ya kamata mu yi? Addu’a ne da zumi muna rokon Allah ya ya zaba mana mafi kyau. daya daga cikin babban hidiman da za ka iya yi domin wannan kasa ita ce, ka samu zarafi ka yi addu’a da azumi, domin wannan kasa tamu. Duk mutumin da za ka iya yi masa addu’a;  ba za ka yi gaba da shi ba. Ra’ayi zai iya bambanta, amma babu gaba ko kuwa kiyayya tsakanin ku. Lokacin kuwa yanzu ne.
Allah bai ba mu kayyadadden lokaci na yin azumi ba, wato za mu iya yin azumi a ko yaushe, Allah bai ba mu yawan kwanakin yin azumi ba, zai iya zama na kwana daya, ko kuwa biyu ko kwanaki uku, ko mako daya ko wata biyu ko wata uku, ya danganta ga abin da ka shirya tsakanin ka da Allah. Dole ne mu samu lokaci na yin addu’a da azumi, domin wannan kasa idan har muna son zaman lafiya. daya daga cikin rokon da zamu yi kuwa shi ne – Allah ya cika zuciyar mutane da tsoronsa. Tushen yawancin damuwar mutum; ba wani abu  ba ne, rashin tsoron Allah ne, idan ka ga wani wanda yake tsoron Allah, zai yi abu daidai, idan ka ga wata wadda ke tsoron Allah, za ta yi abu daidai;  sai mu lura irin wannan ba kawai ka fata za a same su ba ne, a’a, rokon Allah ne ya ke kawo su. Kada mu gaji, mu yi namu fanin, ta wurin yin addu’a sai mu bar wa Allah sauran,  Shi ya san abin da zai yi.
Ubangiji Allah ya ci gaba da tsare mu daga dukan nufin miyagu. Amin.