✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Azaba ce ta sa suka amsa laifin Boko Haram a Dubai’

Ana zaluntar 'yan Najeriya ko 'yan Kasuwa dake kasashen waje saboda sakacin gwamnatin Najeriya.

Iyalan wasu ’yan Najeriya da aka yanke wa hukunci kan zargin alaka da kungiyar Boko Haram sun ce su aka yi suka amsa laifin da ba su aikata ba.

Wata kotu a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ce ta yanke wa ’yan Najeriyan hukuncin da ’yan uwan nasu ke ganin babu adalci.

Yusuf Ali Yusuf dan uwan Ibrahim Ali Hassan da Bashir Ali Yusuf wadanda kotun ta yanke wa hukuncin daurin shekaru 10 ya shaida wa wakilinmu cewa, “Ibrahim yana harkar canjin kudi kuma yana da rajista da hukumar Dubai.

“Yana kasuwaci da mutane da dama sannan yana ajiyar kudaden mutane, wanda daga ciki yana tura kudi Hong Kong, China da sauransu”.

Yusuf ya kara da cewa an tursasa daya daga cikin ’yan Najeriyan da ake zargi mai suna Surajo ne ya amsa laifin da bai aikata ba, aka kuma yi masa romon-baka cewa ya nuna abokan huldarsa.

Ta haka ne, a cewarsa, aka kama Ibrahim da Bashir, aka azabtar da su, aka tursasa su amsa laifin da kotun ta daure su shekara goma-goma a kai.

Dadewar da suka yi a tsare

Yusuf ya bayyana wa wakilinmu cewa, “An kama su a Afrilun 2017 sannan suka shafe shekara daya da rabi kafin daga baya aka fara shari’a.

“Sun shafe wata shida a hannun hukumar farin kaya ta SSS sannan suka yi zaman wakafi na shekara daya a gidan yari”, inji Yusuf.

Ya ce a zaman kotun an ki ba su damar yin magana ballantana su kare kansu daga tuhumar da ake musu.

A cewarsa, Surajo da Saleh kadai aka ba damar magana a kotun; a zaman farko Surajo bai ce komai ba sai a zama na gaba ya shaida wa kotun cewa tursasa shi jami’an tsaro suka yi, amma duk da haka kotun ya yanke hukunci.

Tsakanin iyalansu da gwamantin Najeriya

Ya ce tun da aka fara shari’ar suke fafutukar ganin hukumomi masu alhaki a Najeriya sun bibiyi lamarin don tabbatar da anyi wa ’yan uwan nasu adalci.

Kamar yadda ya ce, sun je Ma’aikatar Harkokin Kasashen Waje, sun sha ganawa da tsohuwar Minista a Ma’aikatar, Khadija Bukar Abba Ibrahim a wancan lokaci, ta kuma ba su tabbacin gwamnati za ta yi duk abin da ya dace na ganin an sake su.

Ya ce sun kuma gana da Ministan Shari’a Abubakar Malami a kan lamarin, ya ba su tabbacin yin iya bakin kokarinsa, amma daga baya sai ta kasance ba sa samun ganin sa idan suka je ofishinsa a kan batun.

Daga bisani suka kai koke Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osibanjo, inda aka ba su kwarin gwiwar za a yi kokarin ganin komai ya kammala cikin ruwan sanyi.

Da aka tuntube shi, Ministan Shari’a Abubakar Malami, ya shaida wa manema labarai cewa ofishinsa na da masaniya a kan lamarin.

Malami ya ce sun tura wa hukumomin Dubai bukatar a turo wa Najeriya kundin binciken da shari’ar da aka gudanar kan ’yan Najeriyan.

Amma shiru (UAE) ba ta turo wa gwamnatin Najeriya sakamakon binciken nasu ba.

Mahangar jama’a

Ammar Aminu ya yi zargin sakacin gwamnati ne ke sa ake wa ’yan Najeriya mazauna kasashen waje kazafi a kuma hukunta su a kai.

“An dade ana yanke wa ’yan Najeriya hukucin sharri saboda rashin gatansu, wanda mafi yawa daga cikinsu ba su aikata laifin da ake tuhumarsu da shi ba”, cewarsa.

Ibrahim Aliyu Usman (Shanee) dan canji a kasuwar Wapa da ke Kano, na shakkar cewa wadanda aka yanke wa hukuncin za su aikata abin da ake zargin su.

“Na zauna da su tsawon shekaru muna huldar kasuwanci, mutane ne masu rikon amana da gaskiya, babu abin da zai sa su aikata laifi makamancin wannan”, inji Shanee.

Mubarak Mustapha kuma cewa ya yi wannan batu ne da ke bukatar bincike na tsanaki saboda ya shafi ta’addanci.

A nasa bangaren, Usman Usman na ganin idan har an tabbatar suna da alaka da ’yan Boko Haram to hukuncin da aka yanke ya yi.

Wasu kuma na ganin in har gaskiya ake nema, to abin da ya fi dacewa shi ne a dawo da su Najeriya a ci gaba da shari’ar saboda a nan ake rikicin Boko Haram ba a Dubai ba.

Fahimtar lauyoyi

Barista Habibu Ma’aruf, lauyan Ibrahim da Bashir, ya ce sakacin gwamnati ne ke jefa ’yan Najeriyan cikin tsaka mai wuya a kasashen waje.

“Dubai ba ta yi adalci ba domin wanda ake zargin ba a ba su damar yin bayani ba, ballantana damar gabatar da shaidu.

“Kotun ba ta bayar da wasu dalilai da suka nuna suna mu’amala da ’yan Boko Haram ba.

“Amma gwamnatin Najeriya za ta iya bin hanyar diflomasiyya wurin warware wannan lamari”, cewar Barista Ma’aruf.

Ya ce dole ne gwamnatin Najeriya ta rika ba ’yan kasarta mazauna ko ’yan kasuwa a kasashen ketare kariya daga hukucin da ake yanke musu ba bisa hakki ba.

“Dole sai gwamnati ta ba wa ’yan Najeriya da ke kasashen waje kariya, saboda irin wannan ya faru da wata yarinya a kasar Saudiyya”, inji shi.

Barista Bulama Bukarti

Barista Bulama Bukarti lauya ne mai zaman kansa kuma mai bincike a kan ayyukan Boko Haram a Najeriya, ya ce akwai lauje cikin nadi game da shari’ar.

“Tun da na karanta wannan labari zuciyata ke min kaikayi a kan wasu abubuawa.

“An ce wadannan mutane suna tura wa wakilan Boko Haram kudi ne a Najeriya.

“Amma kuma ta tabbata cewa ita Hadaddiyar Daular Larabawa ba ta hada kai da gwamnatin Najeriya wajen yin bincike tare da gano su wa ake tura wa kudin ba”, inji Bukarki.

Ya kara da cewa ko da gwamnatin Najeriya ta gamsu da hukuncin da aka yanke, yana da kyau ita ma ta yi nata binciken domin tabbatar da gaskiyar lamarin.

Idan kuma ta gano ba a yi wa ’yan kasarta adalci ba, sai ta kwatar musu hakkinsu ta hanyar diflomasiyya.

Masu sharhi na ganin gwamnanti na bukatar ta sa ido kan yadda ake tauye hakkin ’yan Najeriya ba bisa ka’ida ba a kasashen ketare da sunan hukunci.

Rashin hakan ke kai wa a daure ’yan kasar ko a zartar musu da hukuncin kisa a kasashen waje saboda laifukan da ba su aikata ba.

Tunda lamari ne da ya shafi ta’addanci, babba ne, kuma tsaron al’ummar kasa, Najeriya na bukatar ta ba da muhimmanci ga harkar bincike da hukunta masu laifi da kuma tabbatar da adalci ga wadanda ake zargi.

Kar a koma ‘yar gidan jiya

A irin hukunci da ake yankewa ’yan Najeriya a ketare ne a 2019 aka kusa kashe wata daliba a Jami’ar Yusuf  Maitama Sule da ke Kano, Zainab Habib Aliyu.

Bayan Saudiyya ta yanke wa Zainab hukuncin kisa bisa zargin safarar kwayoyi ne matasa suka yi zanga-zangar lumanar goyon bayanta da jan hankalin gwamnati ta bibiyi lamarin.

Najeriya ta kafa kwamitin da ya kai ga tseratar da dalibar bayan zurfafa bincike da ya gano cewa wasu ma’aikatan filin jiragi na Malam Aminu Kano ne suka sa kwayoyi a cikin kayanta a hanyarta ta zuwa Saudiyya yin Umrah.

Don haka wasu ke ganin shi ma hukunci da aka yanke wa wadannan ’yan Najeriya a UAE bisa zargin tura kudi domin taimaka wa Boko Haram a Najeriya, ba mamaki irin abin da ya nemi ritsawa da Zainab ne.