✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

Ayyukan ’yan bindiga ya ragu matuka a Katsina – Masari

Ya ce babu wani suddabaru da ya yi amfani da shi wajen samun nasarar.

Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya ce babu wani suddabaru da ya yi amfani da shi wajen rage yawan satar mutane da aikata laifuka a Jihar.

Masari ya bayyana hakan ne lokacin da yake amsa tambayoyin tawagar Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Katsina ranar Lahadi.

Ya ce masu rike da sarautun gargajiya da jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki a dukkan lungu da sakon Jihar yanzu na taka muhimmiyar rawa wajen lalubo bakin zaren matsalar tsaron da ta addabi Jihar.

A cewarsa, “Na ba da umarnin cewar dukkan mutanen kirki da ke zaune a dazuka su fito su shiga cikin sauran al’umma a kauyuka da manyan garuruwa da birane don gudun yi musu kudin goro.

“Saboda haka, yanzu ba mu da sauran mutanen da ke zaune a daji. Duk wanda ka gani a daji yanzu to ko dai dan bindiga ne ko kuma bata-gari,” inji Gwamnan.

Masari ya kuma ce Gwamnatin Jihar za ta gina gidaje domin sake tsugunar da mutanen da ayyukan ta’addancin ya raba da muhallansu.

“A zahirin gaskiya, hatta tsofaffin da har yanzu suke cikin daji su ma ’yan bindiga ne wadanda ke fitowa su aikata ta’asa sannan su koma, mun cimma nasara sosai wajen magance matsalar tsaro a Jiharmu,” inji Masari.

Ya kuma lura cewa tabbatar da zaman lafiya a Jihar alhaki ne da ya rataya a wuyan kowa ba gwamnati kadai ba. (NAN)