Tabarbarewar harkar tsaro a Arewacin kasar nan ba sabon abu ba ne, musamman ma ganin yadda ayyukan ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane ke kara tsananta a jihohin Arewa maso Yammacin kasar wadanda suka hada da Jihar Katsina da Jihar Zamfara da wani yanki na Jihar Kaduna.
Sai dai a ’yan kwanakin nan lamarin ya fara kutsawa Jihar Kano, inda a da can ba a cika samun lamarin ba, domin ko a makonnin da suka gabata an sace matar Dagacin garin Tsara da ke yankin Karamar Hukumar Rogo a cikin jihar inda ta shafe wasu kwanaki a hannun masu garkuwa da ita kafin daga baya ta shaki iskar ’yanci bayan iyalanta sun biya kudin fansa.
- Pantami zai yi magana da Buhari kan yankan rago da aka yi wa manoma 43 a Borno
- Harin Zabarmari: Buhari ya jajanta kan kisan manoma 43
A makon da ya gabata ma a ranar 17 ga watan Nuwamba 2020 sai da Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta kama wani matashi mai suna Saleh Habib wanda ya yi garkuwa da wata yarinya mai suna Asiya Tasi’u ’yar kimanin shekara takwas da haihuwa a Karamar Hukumar Gabasawa wanda daga baya kuma ya hallaka ta bayan ya karbi kudin fansa Naira dubu 500 daga iyayenta.
A ranar Lahadin da ta gabata 22 ga watan Nuwamba 2020 kuma an samu rahoton yadda wasu ’yan bindiga suka kashe wani dattijo mai suna Malam Nuhu Muhammad a garin Tumfafi a yankin Karamar Hukumar Garko, inda suka cire kansa tare da sassara dansa wanda ya biyo bayansu da niyyar daukar fansar mahaifinsa.
Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa ba wanann ne karo na farko da ’yan ta’adda ke kai wa dattijon hari ba domin tsawon watanni biyu da suka gabata an kai masa makamancin wannan harin inda suka yi masa barazanar za su kone gidansa gaba daya.
Har ila yau kuma a tsakar ranar Litinin da ta gabata, wato ranar 23 ga watan Nuwamba 2020 an sace wakilin Dagacin Tofai a yankin Karamar Hukumar Gabasawa a jihar mai suna Babawuro Tofai wanda kuma kani ne ga Ministan Ayyukan Gona Alhaji Sabo Nanono kamar yadda wani mataimaki na musamman ga ministan mai suna Umar Wali ya tabbatar.
A cewar Umar Wali har zuwa wannan lokaci ba su ji daga wurin wadanda suka yi awon gaba da dan uwan ministan ba.
Shi dai Babawuro ya samu damar rike wakilcin Dagacin ne biyo bayan nadin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi wa wansa Alhaji Sabo Nanono a matsayin Ministan Ayyukan Gona wanda shi ne Dagacin garin na Tofai.
Rahotanni sun bayyana cewa ’yan bindigar wadanda yawansu ya kai 10 sun raunata wani daga cikin ’yan uwan ministan kafin su yi awon gaba da Wakilin Dagacin.
Akwai sauki a Jihar Kano – Rundunar ’yan sanda
Aminiya ta tuntubi Kakakin Rundunar ’yan sandan Jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewa rundunar tana kokari wajen ganin an tabbatar da tsaro a jihar tare da bibiyar sawun masu aikata ta’addanci a jihar.
“Idan kun duba Jihar Kano tana daya daga cikin jihohin da ta yi iyaka da johohin da ake samun rashin tsaro amma akwai saukin faruwar wadanann lamurra a jihar duk da cewar a ’yan kwanakin nan ana samun faruwar wasu lamurra amma rundunar ’yan sanda karkashin jagoranci Habu A. Sani tana yin kokari wajen dakile rashin tsaro a jihar tare da kokarin bin diddigin wasu abubuwa na rashin dadi da suka faru don gano wadanda ke da hannun a cikin lamarin.
Idan kun duba ko a makon jiya mun yi nasarar kama wani matashi da ya yi garkuwa da wata yarinya wanda aka dauki tsawon lokaci muna bibiyarsa tun daga nan Kano da Kaduna da Abuja da Abiya har dai ya dawo Jihar Kano inda muka kama shi.
Jami’anmu na aiki dare da rana don ganin sun bankado asirin masu aikata ayyukan ta’addanci a jihar ko kuma masu fakewa a jihar.”