A gobe Asabar ake sa ran za a yi wasan karshe a gasar cin Kofin Kwallon Kafa ta Mata ta Afirka (AWCON), a tsakanin kungiyar kwallon kafa ta mata ta Najeriya, Super Falcons da takwararta ta Afirka ta Kudu, Bayana-Bayana. Wasan zai gudana ne da misalin karfe 6 na yamma agogon Najeriya a kasar Ghana wadda ta dauki nauyin gudanar da gasar a wannan karo.
Kafin kungiyoyin biyu su kai wannan mataki, Kungiyar Super Falcons ta samu nasara ce a kan ta Kamaru da ci 4-2 a bugun finareti bayan an kwashe kimanin minti 120 ba tare da kowace ta zura kwallo a raga ba.
Ita kuma Afirka ta Kudu ta samu nasarar kaiwa wasan karshe ne bayan ta lallasa takawararta ta Mali da ci 2-0.
Wani abin lura shi ne duk yadda ta kaya a wasan goben, dukan kungiyoyin biyu sun haye zuwa gasar cin Kofin Kwallon Kafa ta Mata ta Duniya da za a gudanar a Faransa a badi (2019).
Idan za a tuna Afirka ta Kudu ta lallasa Najeriya a wannan gasa da ci daya mai ban haushi a wasan farko a rukunin B, sai ga shi ta sake hada su a wasan karshe da za a yi gobe.
Masana harkar kwallo sun ce wasan zai yi zafi, ganin Najeriya za ta yi kokarin rama cin da aka yi mata yayin da Afirka ta Kudu kuma za ta nemi kafa tarihi wajen lashe wannan gasa a wannan karo.
Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) tuni ta biya ’yan kwallon Falcons hakkokinsu don ganin sun samu karfin gwiwar doke Afirka ta Kudu a wasan gobe.
Ana gudanar da wannan gasa ce duk bayan shekara 2, kuma tun bayan kirkirota a 1998, Najeriya ce ta fi yawan lashe gasar, inda kawo yanzu ta lashe sau 8.