✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Auren Marayu: Limamai sun yi wa Ministar Tinubu wankin babban bargo

Shugaban majalisar, Barista Abdulmalik Sarkindaji, ya ce bai ji dadin yadda ministar ta tozarta shi ba.

Gamayyar kungiyoyin addinin musulunci da ta limaman Jihar Neja sun yi wa Ministar Mata, Uju Kennedy-Ohanenye tofin Allah-tsine bayan ta yi yunkurin hana shugaban majalisar jihar yi wa wasu ’yan mata marayu guda 100 auren gata. 

Bayan furucin na ministar kan cewa za ta kai karar Barista Abdulmalik Sarkindaji kotu muddin bai fasa shirin aurar da ’yan matan ba, tuni ya janye jikinsa, yana mai cewa ya bar ta da limamai da kuma sarakunan gargajiyar jihar su yi musu alkalanci.

Sakataren kungiyar gamayyar malamai da limaman Jihar Neja, Umar Abdullahi yayin wani zama na gaggawa da aka kira a birnin Minna, ya ce kalaman na ministar, batanci ne garesu, a matsayinsu na malamai kuma limaman addinin musulunci a jihar.

Limaman sun bukaci ministar ta fito ta bada hakuri a fili ba a boye ba, kuma ta bayyana tubar ta da janye maganganunta nan da kwananki bakwai.

Limaman sun ce mai irin wannan tunani na Ministar Mata ba ta cancanci zama minista a kasar da ke al’umma masu fahimta iri daban-daban ba.

Da yake bayyana zare hannunsa daga batun auren marayun, shugaban majalisar, Barista Abdulmalik Sarkindaji, ya ce bai ji dadin yadda ministar ta fito ta tozarta shi ba.

Ya ce, ba ta tuntube shi ba kafin ta fito tana masa barazana har da kiran zata kai shi kotu in bai janye ba.

Barista Abdulmalik ya ce magabatan yaran da shugabannin addinin musulunci sun gabatar masa da ‘yan mata 270, daga bisani ya tantance ya wari 100 domin farawa da su.

Kawo yanzu dai a ciki da wajen Jihar Neja ministar na ci gaba da shan suka da caccaka daga wurin musulmi, inda har wasu ke cewa wannan furuci nata cin miutuncin addinin musulunci ne.