Kusoshin jam’iyyar APC sun yi tsinke wajen halartar daurin auren dan tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, wanda ya auri diyar tsohon Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), Malam Nuhu Ribadu.
Mahalarta daga bangarorin siyasa da sassa daban-daban ne suka halarci daurin auren ciki har da jagororin jam’iyyun da manyan jami’an gwamnati masu ci da tsofaffi da sauran manyan ’yan siyasa.
Tun kafin zuwan ranar ’yan Najeriya ke kallonsa a matsayin aya game da rashin dacewar nuna wa juna kiyayya saboda bambancin siyasa ko jam’iyya.
Bayan daura auren Aliyu Atiku da amaryarsa Fatima Ribadu a Abuja a ranar Asabar ne Atiku, dan takarar Shugaban Kasa a Jam’iyyar PDP a zaben 2019 ya wallafa hotunan ma’auratan.
Ya kuma nuna godiya ga mahalarta daurin auren da suka hada da tsohon Shugaban Kwamitin Amintattun jam’iyar APC, Cif Bisi Akande da uban jam’iyyar na kasa, Bola Ahmed Tinubu da Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje da takwaransa na Jihar Yobe, Mai Mala Buni da sauransu.
Iyayen amarya da angon, wadanda dukkanninsu ’yan Jihar Adamawa ne amma daga jam’iyyu masu adawa da juna, sun yi aiki tare a lokacin mulkin tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo.
Atiku shi ne Mataimakin Shugaban Kasa, Malam Nuhu Ribadu shi ne shugaban EFCC, a lokacin shi kuma Tinubu yana gwamnan Legas.
Atiku da Ribadu sun dade suna takun saka tun a lokacin Obasanjo, inda Ribadu ya amsa bukatar Hukumar Binciken Laifuka ta Amurka (FBI) na bincikar Atiku da dan Majalisar Dokokin Amurka, Thomas Jefferson bisa zargin rashawa a wata badakalar man fetur.
Binciken na EFCC bai samu Atiku da laifi ba, amma ya bankado wani zargin facaka da kudin gwamnati a Asusun Albarkatun Man Fetur (PTF) wanda ke karkashin kulawar Atikun.
Tun bayan barinsu gwamnati, Atiku da Ribadu suke yin jam’iyyu masu Adawa da juna.
Tun gabanin daurin auren wasu ’yan Najeriya ke ta yin tsokaci ganin yadda bambancin siyasa bai hana hulda da auratayya tsakanin iyalan ’yan siyasar masu adawa da juna ba.