Kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid ta ci gaba da jan ragamar gasar Laliga, bayan ta doke kungiyar Sevilla a daren ranar Talata.
Sevilla ta sha kashi ne a hannun Atletico Madrid da ci 2-0, ta hannun ’yan wasanta Angel Correa da kuma Saul Niguez.
- Kano Pillars na neman dan wasanta ruwa a jallo
- Almajirai sun daina bara a Kebbi
- COVID-19: A rusa gidajen dambe da na rawa 5 a Abuja
- Kotu ta yanke wa soja hukuncin kisa ta haryar harbi
Atletico Madrid na da maki 41 daga wasanni 16 da ta buga a gasar, inda ta ba wa Real Madrid tazarar maki 4 daga wasanni 18 da ta buga.
Kieran Trippier ya dawo buga wa Atletico Madrid wasa, bayan da Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) ta dakatar da shi wassani 10, saboda karya ka’idojin caca.
Atletico Madrid na da damar kara ba da tazarar maki tsakaninta da Real Madrid, a yayin karawarta da Eibar a karshen wannan satin.
Real Madrid da Barcelona ba za su buga wasa a karshen wannan mako ba, saboda za su buga gasar Spanish Super Cup.