✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Atiku ya ziyarci Kano saboda komawar Shekarau PDP

Yanzu nan na sauka a Cibiyar Kasuwanci.

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya isa Jihar Kano saboda bikin karbar tsohon gwamnan jihar Malam Ibrahim Shekarau daga jam’iyyar NNPP.

Cikin wani sako da tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ya wallafa a shafinsa na Twitter a Lahadin nan, ya bayyana cewa, “yanzun nan na sauka a Cibiyar Kasuwanci, Kano.

“Za mu gudanar da abubuwa da yawa cikin ’yan kwanaki masu zuwa wadanda za mu ribatu da su.”

Ziyarar tsohon Mataimakin Shugaban Kasar na zuwa ne a adaidai lokacin da ake dakon jin matsayar Sanata Shekarau da tun a makon da ya gabata ake jita-jitar tsamin dangartaka da za ta shi ficewa daga jam’iyyar NNPP.

Wata majiya da ke da kusanci da Malam Shekarau ta shaida cewa a ranar Litinin ce Atiku zai karbi Shekarau a hukumance bayan bangaren tsohon gwamnan ya amince da zawarcin da dan takarar ya gabatar masa.

Shekarau ya dauki matakin komawa PDP sakamakon abin da ya kira  “yaudararsu” da dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar NNPP,

Shekarau ya yi ikirarin cewa jagoran jam’iyyar NNPP bai yi musu adalci ba dangane da yarjejeniyar da suka kulla kafin komawarsa jam’iyyar.

Tawagar Atiku da ta ziyarci birnin Dabon ta hada da abokin takararsa, Gwamna Ifeanyi Okowa na Jihar Delta da kuma Shugaban PDP na Kasa, Iyorchia Ayu.

A farkon wannan makon mai karewa tsohon gwamnan kuma Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, ya nuna alamonin raba gari da jam’iyyar NNPP.

Atiku a Kano
Atiku a Kano
Atiku a Kano

Sanata Shekarau a wata hira da ya yi da BBC ya zargi jagoran NNPP kuma dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar, Sanara Rabi’u Musa Kwankwaso da yaudararsu.

Bayanai sun ce ziyarar da Atiku ya kai Jihar Kanon na daya daga cikin shirye-shiryen ayyana sauyin shekar da Shekarau din zai yi zuwa jam’iyyar PDP a hukumance a ranar Litinin.

Duk da kasancewar Shekarau dan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya a jam’iyyar NNPP, zai hakura da tikitin ya sauya sheka zuwa PDPn domin kara tumke damara da samun goyon bayan karbuwar jam’iyyar a Arewa maso Yammacin kasar yayin Zaben 2023.

Da yake magana da Aminiya, Shugaban PDP na Jihar Kano, Shehu Wada Sagagi wanda ya ziyarci Shekarau a ranar Asabar, ya shaida wa wakilinmu cewa Shekarau ya amince zai sake komawa jam’iyyar ta PDP.

“Allah mun gode maka, a yanzu mun samu jagora a Kano kuma muna farin ciki.

­“Shekarau wanda shi ne mai rike da mukami na siyasa mafi girma a bisa tanadin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, mun amince kuma muna maraba da dawowarsa jami’iyyarmu ta PDP.

“A yanzu tuni shirye-shirye sun yi nisa na ziyarar da Atiku Abubakar zai kawo Jihar Kano a ranar Lahadi domin karbar Mallam Ibrahim Shekarau.

“Mun amince za mu yi masa biyayya kuma da Yardar Allah za mu yi nasara.