Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023 mai zuwa, Alhaji Atiku Abubakar ya lashi takobin kawo karshen matsalar tsaron da ta addabi Najeriya.
Atiku ya kuma yi alkawarin yin aiki tukuru wajen hada kan kasar idan har aka zabe shi a matsayin Shugaban.
- ’Yan bindiga sun kashe tsohon Kwamishinan Hukumar Kidaya ta Kasa
- 2023: Dole APC ma ta kai takararta Arewa ko ta riga rana faduwa — Orji Kalu
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da jawabin samun nasara bayan an ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben fid da gwani na Shugaban Kasa na ham’iyyar PDP.
Atiku ya kuma caccaki jam’iyyar APC kan yadda ta sauya nasarorin da jam’iyyar PDP ta samu a lokacin da take rike da madafun iko, inda ya yi alkawarin gyara su idan aka sake zabe a 2023.
Ya ce, “Zan yi taka-tsan-tsan da matsalolin tsaro da muke fuskanta a kasar nan. Na kuma yi alkawarin tunkarar kalubalen tattalin arzikinmu, wanda gwamnatin APC ta jawo. Jam’iyyar PDP ta sanya Najeriya cikin kasashe masu ci gaba da wadata a Nahiyar Afirka.
“Mun aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki da suka kawo ayyukan yi, da wadata a kasar nan. Bayan karbar mulki da Jam’iyyar APC ta yi ta goge duk wadannan nasarori. Shi ya sa na ce yau rana ce mai matukar tarihi da gaske. Domin hakan zai ba mu dama mu gyara duk wani rashin shugabanci na gwamnatin APC.”
Sai dai ya nemi hadin kan sauran masu neman takara a zaben, inda ya kara da cewa babban abin da ya fi mayar da hankali a kai shi ne kokawa da mulki daga jam’iyyar APC mai mulki.
Atiku ya ce, “Bari ni ma na yi amfani da wannan damar wajen kira ga ’yan takara na. Kuma in tabbatar musu da cewa, a shirye nake na ba su hadin kai da yin aiki da su da kuma ba su fahimtar kasancewa cikin wannan jam’iyya da kuma gwamnatinmu ta gaba.
“Saboda haka ’yan uwana, ina son in yaba da kokarinku na zurfafa tsarin dimokuradiyya a wannan jam’iyya. Zaben fidda gwani ne mai inganci. Don haka, na yaba muku a kan hakan kuma ina fatar yin aiki tare da ku sosai. Ta yadda tare za mu gina wannan jam’iyyar zuwa matakin da za mu iya kwace mulki.”
Ya kuma yi kira ga ’yan jam’iyyar da suka fusata da su guji kai al’amuran jam’iyyar a kotu.