✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Atiku ya lashe zaben shugaban kasa a Yobe

Atiku ya samu Kuri'u 198,567, dan takarar APC Bola Ahmed Tinubu ya samu Kuri'u 151,459.

Atiku ya samu Kuri’u 198,567, dan takarar APC Bola Ahmed Tinubu ya samu Kuri’u 151,459 a zaben shugaban kasa a Jihar Yobe.

Jihar Yobe ita ce mahaifar Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan da kuma tsohon shugaban kwamitin rikon kwarya na Jam’iyyar APC, Gwamna Mai Mala Buni.

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sanar a safiyar Litinin cewa jam’iyyar PDP da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku ke takara ta lashe zaben shugaban kasa a Jihar Yobe da Kuri’u 198,567.

Dan takarar Jam’iyyar APC mai mulki kuma, Bola Ahmed Tinubu ya samu kuri’u 151,459.