✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Atiku ya lashe zabe a Adamawa

Atiku ya yi nasara a 20 daga cikin kananan hukumomi 21 da ke fadin Jihar Adamawa

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya lashe zaben shugaban kasa a Jiharsa ta Adamawa da rata mai yawa.

Sakamakon da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sanar ya nuna Atiku, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na jam’yyar adawa ta PDP, ya yi nasara a 20 daga cikin kananan hukumomi 21 da ke fadin jihar.

Shugaban INEC na Jihar Adamawa, Farfesa Mohammed Mele, ya bayyana cewa jamiyyar PDP ta samu kuri’u 417,611, APC  ta samu 182,881, sai LP mai 105,648, sannan NNPP 8,006 a jihar.

Yea kara da cewa hukumar ta tantance mutune 764,834 daga cikin mutum 2,186,465 da ke da rajistar zabe a jihar Adamawa.