✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Atiku ya kayar da Tinubu a Katsina

Jam'iyyar PDP ta kayar da APC a Jihar Katsina, mahaifar Shugaba Buhari

Dan takarar shugaban kasa na babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar, ya yi nasara a Jihar Katsina, mahaifar shugaban kasa Muhamamdu Buhari.

Sakamakon zaben shugaban kasa da baturen zabe na Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) na Jihar Katsina, Farfesa Mu’azu Abubakar Gusau, ya sanar a safiyar Litinin ya nuna Atiku ya yi nasara da kuri’u 489,045 a yayin da Tinubu na APC ya zo na biyu da kuri’u 482,045.

Kabiru Gaya ya fadi zabe bayan shekara 16 a Majalisa

Yau INEC za ta ci gaba da karbar sakamakon zaben shugaban kasa a Abuja

Hakan na zuwa ne kwana daya kacal bayan Shugaba Buhari ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa dan takarar shugaban kasa na jam’yyarsa ta APC, Bola Tinubu, ne ya zai ci zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar Asabar.

Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar NNPP kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso, ya zo na uku da kuri’u 69,385 sai Peter Obi na Jam’iyyar LP ya zo na hdudu da kuri’u 6,376.

Baturen zaben jihar ya ce a fadin jihar mai kananan hukumomi 34, an soke zabe a wasu rumfuna a kananan hukumomi 15 saboda rikicin siyasa da aringizon kuri’u da sauransu.

A zaben Majalisar Dokoki ta Kasa kuma, jam’iyyar APC mai mulki ta lashe kujerun santa uku da ke jihar da kuma ara cikin kujeru 15 na majalisar wakilan jihar, PDP ta samu shida.