✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Atiku ya jagoranci zanga-zangar neman INEC ta soke zaben shugaban kasa

Atiku da jiga-jigan Jam'iyyar PDP na son INEC ta soke zaben shugaban kasa da aka gudanar.

Dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar da Shugaban jam’iyyar, Iyorchia Ayu, sun jagoranci jiga-jigan jam’iyyar gudanar da zanga-zanga neman a soke zaben shugaban kasa da aka gudanar.

Masu zanga-zangar da suka sa bakaken kaya sun fara taruwa ne a ofishin jam’iyyar, daga nan suka fara tattaki zuwa  Hedikwatar Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da ke Maitama a Abuja.

Abiye Sekibo, Dino Melaye, da Uche Secondus na daga cikin jiga-jigan jam’iyyar PDP da aka hanga a wajen zanga-zangar.

INEC dai ta ayyana Bola Ahmed Tinubu na Jam’iyyar APC mai mulki a matsayin zababben shugaban kasa.

Sai Atiku Abubakar na PDP a matsayi na biyu, Peter Obi na LP a matsayi na uku, sai Rabiu Musa Kwankwaso na NNPP ya kare a na hudu.

Duk da matsin lamba da hukumar INEC ke sha da neman soke zaben, Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban hukumar, ya tabbatar da cewar zaben da aka gudanar sahihi ne.