Karo na farko da Atiku Abubakar ya tsaya takarar Shugaban kasa yana sabon ɗan siyasa ne mai shekara 47 a duniya.
Hakan ya faru ne a 1993 lokacin shekararsa huɗu da fara siyasa. Mai gidansa, Janar Shehu Musa ’Yar’aduwa (mai ritaya) ne ya lasa masa zumar siyasa, kuma nan take ya gano cewa akwai bambanci mai yawa a tsakanin siyasar ƙasa da siyasar da ya yi lokacin yana ɗalibi a Makarantar Aikin Tsafta ta Kano inda aka zaɓe shi Shugaban kungiyar dalibai a 1966.
Ita wannan siyasar cike take da cin amana inda aka fara nuna masa ta hanyar tsallake shi wurin zaɓar wanda zai yi takarar Mataimakin Shugaban kasa tare da MKO Abiola. Wannan cin amanar ne yake ta bibiyarsa tsawon rayuwarsa.
Mai shekara 76 a duniya, wannan na iya zama dama ta ƙarshe da zai nemi cika burin da ya jima yana da shi na kasancewa Shugaban kasa.
A shekara 30 da ya yi yana siyasa, Atiku ya yi takarar Shugaban kasa sau biyar. Wannan na shida, na cike da tarnaƙin da ya kasa tsallakewa lokacin da yake kan ganiyarsa.
Atiku ya fara siyasa ce bayan da ’Yar’aduwa ya je ofishinsa a Hukumar Kwastam neman lasisin shigo da wake. Burge shi da wannan jami’in Kwastam ya yi, ya sa ’Yar’aduwa ya gayyaci Atiku zuwa taron siyasa a gidansa da ke Legas.
Ba a jima ba sai Atiku ya ajiye aikin Kwastam a 1989 yana da shekara 43 inda ya taimaka aka kafa ƙungiyar siyasa ta Peoples Front of Nigeria ta ’Yar’aduwa, wacce daga baya ta narke cikin Jam’iyyar SDP kuma can gaba ta shiga PDP a 1998.
A 1991, ya tsaya takararsa ta farko a matsayin Gwamnan Jihar Adamawa amma Shugaban Kasa Janar Ibrahim Babangida ya kawo masa cikas bayan da ya soke zaɓen fi-da-gwani a jihohi da dama ciki har da Adamawa. Sai kuma ya haramta wa Atiku da abokin takararsa Bala Takaya sake tsayawa takarar Gwamna a jihar. Cikin ikon Allah, wannan soke zaɓen ne ya ba shi damar tsayawa takarar Shugaban Kasa bayan shekara biyu tsakani. A 1993, Janar Babangida ya haramta wa ’Yar’aduwa neman takarar Shugaban kasa.
Don haka ya tsayar da Atiku ya nemi sahalewar jam’iyyar a madadinsa. Sai dai ya haɗu da gogaggun ’yan siyasa irin su MKO Abiola da Babagana Kingibe. Atiku ne ya zo na uku a zaɓen fid-da-gwani don haka a zagaye na biyu sai aka buƙaci ya mara wa Abiola baya bisa sharaɗin zai ɗauke shi mataimaki idan ya yi nasara.
Atiku ya amince amma da Abiola ya yi nasara sai ya bai wa Kingibe gurbin mataimakin. Wanann cin amanar ta ɓata wa Atiku rai kamar yadda ya bayyana a littafin tarihinsa mai taken ‘Rayuwata.’
Abubuwan da suka yi tasiri a rayuwar Atiku
Kamar mahaifinsa, Atiku shi ne ɗa ɗaya tilo a gaban iyayensa kuma ya tashi cikin kaɗaici. Wannan kaɗaicin ya ƙara tsananta lokacin da mahaifinsu ya rasu yana da shekara 11 kacal. Mahaifinsa, Garba Atiku Abdulƙadir ɗan kasuwa ne kuma malamin addini da ya gaji mahaifinsa kuma ya so nasa ɗan ya gaje shi.
Sai dai rayuwar Atiku ta saɓa da abin da mahaifinsa ya sa rai. A shekarun 1950 Najeriya na kan hanyar samun ’yancin kai. Karatun boko na samun karɓuwa tare da ƙalubalantar tsarin da aka saba. Amma Garba Atiku Abdulƙadir ya turje masa.
Zuwa 1954, lokacin da ya kamata a sa ɗansa a makaranta, ya ƙi amincewa. Sai ɗan uwansa Aliyu wanda shi ya yi karatun yaƙi da jahilci ne ya kai Atiku makarantar firamare da ke Jada. Saboda Malam Garba ya ƙi yarda ɗansa ya shiga makarantar boko sai da aka kama shi aka ci tararsa.
Da ya ƙi biyan tarar kuma aka ɗaure shi har sai da wani ɗan uwansa ya biya masa Sulai 10 kafin a sake shi. Duk da wannan tataɓurzar, Atiku yana tuna alherin mahaifinsa wanda tare da mahafiyarsa Kande suka tarbiyyantar da shi cikin soyayya da kulawa ta addini.
Shi kuma Atiku yakan taimaka wa mahaifinsa a gona da kula da shanu. “Mahaifina na kallona a matsayin ɗan baiwa. Yana yawan roƙon Allah Ya kare ni, Ya shiryar da ni, kuma Ya ba ni nasara a rayuwa. Na yi imani cewa shi ne tushen duk wata nasara da na samu. Lallai addu’a tana tasiri, babu ko shakka,” in ji Atiku a cikin littafin.
Sai dai dangantakar tasu ba ta yi nisa ba. A 1957 Malam Garba, wanda a lokacin yana da kimanin shekara 40 ya rasu lokacin da yake ƙoƙarin ƙetara Kogin Mayo Choncha da ke bayan garin Toungo. Washegari aka gano gawarsa.
Bayan shekaru da yawa, Atiku ya gina makarantar Islamiyya a wurin da aka binne mahaifinsa domin tunawa da malamin. A lokacin da mahaifinsa ya rasu, an samu sauyi a halayyar Atiku lokacin da ya shiga makarantar sakandaren Lardin Adamawa da ke Yola a 1960. Domin shawo kan kaɗaicin, ya sadaukar da kansa ga ayyukan makaranta da dama sannan ya zama mafaɗaci har aka kusa a kore shi.
Ɗaya daga cikin abokan karatunsa, MGS Samaki OON, wanda ya yi Jakadan Najeriya a Romaniya ya shaida wa Daily Trust cewa “Atiku Abubakar ɗalibi ne mai ƙwazo da kazar-kazar. Yana ba da himma wurin wasanni da dama. Lokacin malamai suna tabbatar da cewa ɗalibai sun bunƙasa ƙwaƙwalwarsu da jikinsu domin su zama dan ƙasa nagari kuma shugabannin gobe. A makarantarmu akwai ɗalibai daga ko’ina cikin Lardin Adamawa. Ya ƙulla abota da yawa kuma har yanzu yana tare da abokansa.”
Baya ga abota, Atiku kamar sauran matasa, musamman wadanda ke fama da rashin mahaifi, ya samu kansa cikin matsala. Wasan da ya fi mai da hankali a kansa shi ne hockey (kwallon gora) kuma a koyaushe za ka same shi yana yawo da sandar hockey a cikin makaranta. Duk lokacin da wani zai ci zalinsa sai ya doka masa sandar. Raɗaɗin rashin mahaifi ya sa wannan shiru-shirun yaron daga Kojoli ya zama mafaɗaci mai yawo da sanda a Yola.
Sai da ta kai wata shida da fara karatun sakandare, shugaban makarantar Dabid West ya gargaɗi Atiku ya daina faɗa ko a kore shi. Ba mamaki a Yola ne Atiku ya koyi zama ɗan gwagwarmaya tsawon rayuwarsa, wanda ya sha kaye a ƙoƙarinsa na neman zama Shugaban kasa amma bai karaya ba, inda yanzu ake ganin yana gwadawa ne a karonsa na ƙarshe.
A 2027 shekarunsa za su zama 80 kuma zai yi wuya ya shiga takarar. Sai dai wa ya san gobe?
Sukuwar Atiku ta ƙarshe?
Tun 2022 Atiku yake faman ɗauki-ba-daɗi da wasu daga cikin ’yan jam’iyyarsa ta PDP, wacce ya taimaka wurin kafa ta a 1998 bayan da ƙungiyar maigidansa ’Yar’aduwa ta NPF ta narke a cikin sabuwar jam’iyyar.
Tun fara siyasarsa yake fama da abokan hamayya. Na farko shi ne Bala Takaya wanda suka sha bugawa kan neman kujerar Gwamnan Jihar Adamawa. Nasarar da Atiku ya taɓa samu a zaɓen duk gari ita ce wacce ya kayar da Takaya a zaɓen 1999. Ya yi nasara amma ba a rantsar da shi a matsayin Gwamna ba. Saboda saɓanin abin da ya faru a 1993, an ba shi damar tsayawa takarar Mataimakin Shugaban kasa ga Janar Olusegun Obasanjo. A zahiri sai a ce haɗin ya yi daidai.
Obasanjo da ’Yar’aduwa sun yi mulki tare daga 1977 zuwa 1979. Kuma bayan rasuwar ’Yar’aduwa an bai wa magajinsa damar maye gurbinsa a wurin tsohon ubangidansa. Abin mamakin shi ne yadda aka rantsar da Obasanjo da Atiku a matsayin Shugaban kasa da Mataimakinsa ranar 29 ga Mayun 1999 amma Obasanjo ya zamo babban mai adawa da Atiku bayan wannan lokaci.
A koyaushe Atiku ya yunƙura Obasanjo ne ke katse masa hanzari. A 2007 lokacin da ya kamata ya gaji Obasanjo, tsohon Janar ɗin ne ya ƙwashe masa ƙafa inda ya zaɓo ƙanin ’Yar’aduwa, Umaru ya maye gurbinsa. Wannan ya faru ne bayan da Atiku ya daƙile yunƙurin tazarcen Obasanjo a karo na uku.
Bayan da aka tilasta masa ya bar jam’iyyar, Atiku ya shiga Jam’iyyar AC, inda ya samu tikitin takarar Shugaban kasa. Amma ya kwashe lokacin neman zaɓe yana fafatawa ne a kotu bayan da Hukumar INEC ta soke takararsa bisa zarginsa da almundahana. Zuwa lokacin da ya samu nasara a kotu, Atiku ya riga ya san aikin gama ya gama.
Ya ce “A wancan lokacin na san cewa idan ban yi takara a wannan zaɓe ba, duk shekarun da na kwashe ina gwagwarmaya sun tashi a banza. A gaba za a iya hana mutane shiga zaɓe saboda ƙiyayyar wani mutum ta take umarnin kotu. Haka kuma na yi takarar ce saboda ko in ci ko in faɗi zan ƙara ƙarfafafa tsarin dimokuraɗiyyarmu ko da kuwa sakamakon bai yi min daɗi ba.
“Don haka washegari, na fita, na kaɗa ƙuri’a, na koma gida na jira faɗuwata kamar yadda na zata. Na san cewa kodayake zan faɗi, a wannan karon ni na yi nasara a yaƙin – wato yaƙin kare tsarin dimokuraɗiyyarmu,” kamar yadda ya shaida wa jaridar Vnguard a wata hira da suka yi cikin shekarar 2013.
Kaso bakwai cikin ɗari kacal ya samu daga ƙuri’un da aka kaɗa ƙasa da rabin abin da Muhammadu Buhari ya samu yayin da wanda ya yi nasara ’Yar’aduwa ya ninka sau shida.
Hana rantsuwa Obasanjo ya sassauta wa Atiku a 2019 inda ya mara masa baya a takararsu da Muhammadu Buhari. Amma dai bai yi wani tasiri ba domin kuwa Atiku faɗuwa ya yi a zaɓen.
A yayin da muke tunkarar zaɓen 2023, saɓanin da ya lafa shekaru huɗu da suka shuɗe yanzu ya dawo da ƙarfinsa.
Obasanjo ya sake buɗe wuta wajen yaƙar Atiku wanda ya kira mai cin hanci da rashawa. Sai dai a wannan karo ba Obasanjo ne kawai matsalar Atiku ba.
Yana ɗauke da tutar PDP ne a lokacin da jam’iyyar ke cikin mawuyacin halin da ba ta taɓa shiga ba tun kafa ta. Bayan ta rasa mulki tsawon shekara takwas, jam’iyyar ta shiga halin ƙaƙa-nika-yi.
Akwai mummunan rikicin cikin-gida a tsakanin Atiku da wanda yake ɗaukar ɗawainiyar jam’iyyar, Gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike wanda Atiku ya kayar a zaɓen fid-da-gwanin da aka gudanar a Mayun 2022, sannan ya ƙi amincewa ya ba shi takarar Mataimakin Shugaban kasa.
Tun daga sannan Wike ke cin dunduniyar Atiku inda ya janwo ƙarin gwamnonin PDP huɗu suke yi wa Atiku tutsu. Baya ga wannan, takarar Atiku, kamar sauran an takarar Shugaban kasa na fuskantar tarnaƙi.
Wasu daga ciki daɗaɗɗu ne, yayin da wasu kuma sababbi ne.
Nauyin akwatuna 53 da ke kan Atiku
A 1984 lokacin da Atiku yake babban jami’in Hukumar Kwastam da ke kula da tashar jiragen sama ta Murtala Mohammed a Legas, zamanin Janar Muhammadu Buhari yana Shugaban kasa kuma ya rufe iyakoki saboda canjin kuɗi, sai ga rahoto ya ɓulla cewa an ƙyale wasu akwatuna 53 sun wuce shingen Kwastam ba tare da an bincike su ba. Lamarin ya zama babbar badaƙala a lokacin kuma har yanzu ana tattaunawa a kai.
A 2017, lokacin ƙaddamar da Gidauniyar Onukaba AdinoOjo, ɗan jaridar da ya bankaɗo labarin a lokacin, Atiku ya tuna yadda lamarin ya kusa ya jawo masa asarar aikinsa.
Buhari ma ya taɓa tuno da labarin a wata hira da aka yi da shi a 2011. Ita ma matar Atiku, Titi Abubakar ta yi maganar a 2018. Taƙaddamar ta taso ne lokacin da dogarin Shugaban kasa Manjo Mustapha Jokolo ya tuƙa motarsa har zuwa titin da jirgi ke tashi, ya jidi wasu akwatuna 53 sannan ya yi tafiyarsa ba tare da ya amince da binciken Kwastam ba.
A cewarsa akwatunan mahaifinsa ne da na iyalan wani jami’in diplomasiyya da suka dawo daga ƙasar waje.
Atiku ya ce laifinsa ɗaya shi ne tabbatar wa ’yan jarida cewa lamarin ya faru, abin da ya jawo har aka kusa korarsa. Yayin da Buhari ransa ya sosu cewa makusantansa na karya dokar da ya ɗora wa sauran ’yan Nijeriya. Wannan shi ne masomin saɓanin da ke tsakanin Atiku da Buhari.
A lokacin Atiku ya tsallake korar amma har yanzu yana fama da zarge-zargen da nauyinsu ya kai na waɗancan akwatunan 53.
Na farko, kamar abokin takararsa Tinubu, ana tababa a kan tushen dukiyarsa. Sai dai Atiku wanda yana da shekara 15 ya saya wa mahaifiyarsa gidan ƙasa lokacin da yake aiki a matsayin akawun wucin-gadi a En’e ta Ganye, ƙarƙashin Adamu Ciroma ya ce ya yi kuɗi ne ta hanyar ƙwarewarsa a kasuwanci.
Ya ce ya ci bashin gwamnati ne a 1974 ya zuba jari a harkar filaye, kuma ya samu gwaggwaɓar riba. Daga nan ya bunƙasa kasuwancinsa ya shiga harkar fetur a farkon shekarun 1980. Sai dai ba kowa ne ya amince da wannan labarin ba. Duk da binciken da aka sha yi masa, musamman ƙarƙashin gwamnatin abokin adawarsa Obasanjo, ba a taɓa samun Atiku da laifin rashawa ba.
A kotun shari’a Atiku ya samu nasara amma a kotun ra’ayin al’umma har yanzu Atiku bai gamsar da mutane ba, kamar dai yadda lamarin yake ga sauran ’yn siyasa da masu riƙe da muƙaman gwamnati.
Atiku ya kasa kakkaɓe zargin da ake masa na cin hanci da rashawa. Masu sukarsa na ganin kawai yana son zama Shugaban kasa ne don ya wawushe rabonsa daga dukiyar ƙasa.
Suna kuma kafa hujja da aƙidarsa ta sayar da kadarorin gwamnati kamar yadda ya sayar da NITEL. Amma Kakakinsa, Paul Ibe ya shaida wa Aminiya cewa “Atiku sai dai ya bunƙasa arzikin ƙasa ta yadda kowa zai samu yalwa.”
Koma me za a ce game da yaƙin neman zaɓensa, Atiku ya fito ne da shirinsa. A lokacin da ya ƙaddamar da takararsa a watan Maris 2022, ya gabatar da kundin manufofinsa mai shafi 117 mai taken “Yarjejeniyata da ’yan Nijeriya” inda ya mayar da hankali kan ɓangarori biyar: haɗin kan ƙasa, tsaro, tattalin arziki, ilimi da kuma miƙa ƙarin iko ga jihohi da ƙananan hukumomi.
Ba duk ’yan takara ne suke da kundin manufofi kamar nasa ba.
“A bayyane take gwamnati ba ta da isassun kuɗi kuma bashi ya yi mata yawa. Don haka wajibi ne gwamnati ta haɗa kai da kamfanoni masu zaman kansu domin warware matsalolin da suka addabe mu,” Atiku ya shaida wa wani taron ’yan kasuwa da editoci a Legas bara.
Manazarta dai sun yaba da ingancin kundin manufofin Atiku. Kundin ya bayyana ƙwarewarsa da kuma shekarun da ya kwashe yana jagorancin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu. Mista Ibe na ganin wannan ne ya sa ɗan takararsa ya cancanci a zaɓe shi duba da nasarorin da ya samu a fannin kasuwanci da kuma shekara takwas da ya kwashe yana Mataimakin Shugaban kasa.
Sai dai a baya-bayan nan wani mutum mai suna Michael Achimugu wanda ya yi iƙirarin shi hadimin Atiku ne ya fallasa wata badakala da ta jawo ce-ce-ku-ce.
Mutumin ya ce Atiku ya yi amfani da wasu kamfanoninsa ne wajen karkatar da dukiyar al’umma ba tare da an gane shi ba. Achimugu ya kafa hujja da wani sauti ɗauke da murya sak irin ta Atiku yana bayanin yadda ake haɗa irin wannan badaƙalar. “Hirar da Atiku ya yi da shi ta gaske ce,” in ji Mista Ibe.
“Amma me ya kai shi naɗar wannan maganar in ba dama yana nemansa da sharri ba?” Kamar Dino Melaye, Daraktan Hulɗa da Jama’a na Kwamitin Kamfen Shugaban kasa na PDP, Mista Ibe ya ce Achimugu bai taɓa zama hadimin Atiku ba, kawai dai ɗan kore ne.
“Wannan tsari ne da ake yin sa a faɗin duniya. Kuma an buɗe kamfanonin ne saboda a gudanar da ayyukan jam’iyya ba tare da an kwashe kuɗin gwamnati ba. BabUwani sabon abu kan maganganun da ya yi don haka bai kamata kowa ya damu ba,” in ji Mista Ibe.
Karɓa-karɓa
Ɗaya daga cikin manyan matsalolin Atiku a wannan zaɓen shi ne kasancewarsa ɗan Arewa. Bayan shekara takwas na mulkin Buhari, wanda shi ma ɗan Arewa ne, kuma Atiku ya taimaka aka zaɓe shi Shugaban kasa a 2015, abin da aka saba shi ne mulki ya koma Kudu.
APC ta zaɓi ɗan takara daga Kudu maso Yamma yayin da LP ta zaɓo nata daga Kudu maso Gabas. Kasancewarsa ɗan Arewa na daga cikin abubuwan da suka sa nasararsa a Jam’iyyar PDP ta jawo ce-ceku-ce.
Tun daga rasuwar Shugaba ’Yar’aduwa a 2010 da maye gurbinsa da Goodluck Jonathan daga Kudu tsarin karɓa-karɓa na Jam’iyyar PDP ya samu tasgaro.
A 2022 bayan da aka kai ruwarana, PDP ta yanke hukunci buɗe damar takara ga dukkan sassan Najeriya. Mista Ibe ya ce ceto Nijeriya ba aikin wani ɓangare ne kaɗai ba kuma Atiku shi ne kawai da zai iya haɗa kan ƙasar nan a wannan lokaci da ake fama da rarrabuwar kai. “Gidan Atiku ƙaramar Nijeriya ce,” a cewar Mista Ibe wanda ke bayyana irin mutanen da ke tururuwa su cika gidansa.
“Shi kaɗai na sani wanda ya san aƙalla mutum guda a duk mazaɓar da ke faɗin ƙasar nan. Ya yawata sosai kuma shi ne zai iya haɗa kan al’umma,” in ji shi.
Ambasada Samaki, abokin Atiku a makarantar sakandare ya ce kaɗaicin da Atiku ya yi fama da shi lokacin ƙuruciya shi ya sa ya zama mutumin jama’a.
“Atiku Abubakar mahaifiyarsa ce ta raine shi bayan rasuwar mahaifinsa yana ƙaramin yaro. Don haka ya yi ƙoƙari kada ya ɓata ran mahaifiyarsa,” in ji Samaki.
“Kasancewarsa ɗa ɗaya tilo ya sa akwai shi da son abokai ba tare da la’akari da bambancin ƙabila ko addini ba. Yana da sauƙin hali kuma ba ya da ɓangaranci. Kana iya ganin haka a cikin gidansa da iyalinsa da ofishinsa da kamfanoninsa, inda kowane ɓangare na ƙasar nan ke da wakilci a cikinsu,” in ji shi.
Kaɗaicin ne ma ya sa Atiku son tara iyali inda ya auri mata huɗu daga sassa daban-daban na ƙasar nan kuma ya haifi ’ya’ya 28.
Daga cikin ’yan takarar bana kusan a ce shi ne ya fi kowa hulɗa da mutanen ɓangarorin ƙasar nan, abin da ke bai wa magoya bayansa ƙwarin gwiwar cewa zai yi nasara a zaɓen.
Sai dai, a bayyane take cewa goyon bayan da Atiku yake da shi ya yi ƙasa a wasu sassan ƙasar nan idan aka kwatanta da 2019 lokacin da yake da matuƙar karɓuwa a Kudu.
A yanzu kuwa ya samu koma-baya saboda manyan batutuwa guda uku. Na farko shi ne ƙyamar da wasu ke yi na ganin wani Bafulatani daga Arewa ya maye gurbin Buhari.
Na biyu kuma shi ne takarar Peter Obi daga Kudu maso Gabas inda suka ba shi ƙuri’a a baya, sai na ukunsa wani saƙon Twitter da aka goge. Lokacin da wasu fusatattun matasa suka kashe wata ɗaliba Kirista a Sakkwato, mai suna Deborah Yakubu bisa laifin ɓatanci ga Annabi Muhammadu (SAW) an wallafa sukar lamarin a shafin tiwita na Atiku.
Amma sai aka goge daga baya. Wannan ya ɓata ran Kiristoci da dama. Mista Ibe ya ce wannan laifinsa ne na ƙashin kansa.
“A ranar badaƙalar Deborah, yana tafiya ne. Ban samu magana da shi ba, sai na yanke shawarar wallafa bayani a shafin Twitter ba tare da amincewarsa ba. Lokacin da na yi ban san cikakken abin da ke faruwa ba. Da ya samu dama, sai muka duba, muka sake nazari, inda aka yanke hukuncin goge rubutun. An yi haka ne don a kauce wa harzuƙa jama’a. Atiku ya jima yana kare ni, amma lokaci ya yi da zan fito in bayyana rawar da na taka a cikin maganar,” in ji Mista Ibe.
Ya ce, “Idan kana shugaba, aikinka shi ne kashe wutar fitina. Kuma shi ne abin da muka yi.” Sai dai da alama wutar nan ta yi tsalle ta kama cunar rigar Atiku, inda ta haɗe da sauran ƙananan da suka addabe shi. Ɗaya daga cikinsu shi ne ɗinke ɓarakar da ke cikin PDP kafin zaɓen.
“Babu wata ɓaraka a cikin jam’iyya,” in ji Phrank Shaibu, wani hadimin Atiku kan yaɗa labarai da aka tambaye shi game da Wike.
“Wannan mutum ɗaya ne kawai yake yaƙi da PDP, kuma Atiku bai mayar da martani ba duk da ɓaɓatun da suke yi saboda har yanzu a shirye yake a daidaita,” in ji shi.
Ko Wike da abokan burminsa za su amince?
Wannan dai lokaci ne zai nuna. Abin dai da kamar wuya amma babu abin da ba zai yiwu ba a siyasa. Ko ya ci ko ya faɗi, ko an ɓata shi ko ba a ɓata shi ba, shari’o’in da Atiku ya shiga sun taka rawa wajen bunƙasa dimokuraɗiyya a Najeriya.
Ɗaya daga cikin manyan nasarorin da ya samu ita ce ta hana tazarcen Obasanjo. Ba mamaki ya yi ne saboda burinsa na zama Shugaban kasa amma dai burin nasa ya dace da buƙatun Najeriya.
Zai iya cewa yanzu ma haka abin yake amma dai zai yi wuya an Nijeriya su amince da hakan.
“Atiku ba ya takara don yana neman mulki. Amma ya zama wajibi a samu wanda zai sadaukar da kansa wajen jagorantar al’umma, shi ya sa yake takara. Maganar ta al’umma ce kuma sun yi imanin Atiku ne zai jagorance su,” in ji Shaibu.
Ko mene ne gaskiyar wannan batu? Ina ga za mu gano haka a gobe, 25 ga Fabrairu.